HausaTv:
2025-04-01@15:50:09 GMT

Al-Burhan: Sudan Ba Za Ta Shiga Tattaunawa Da RSF Ba

Published: 30th, March 2025 GMT

Shugaban majalisar mulkin kasar Sudan kuma kwamandan Sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan ya tabbatar da cewa, farin cikin samun nasara a Sudan ba zai cika ba har sai an kawar da tungar karshe ta mayakan RSF a kasar, yana mai jaddada cewa kasar ba za ta ja da baya ba har sai an murkushe wadannan mayakan ‘yan tawaye, wadanda suka aikata munanan laifuka kan al’ummar Sudan.

Al-Burhan ya yi nuni da cewa, za a ci gaba da gwabzawa har sai an samu cikakken adalci, yayin da ya tabbatar da cewa ya tsaya tsayin daka da dukkan ‘yan kasar, kuma ya yi imani da ci gaba da kokarin maido da tsaro da kwanciyar hankali a kowane sako  na kasar Sudan.

Al-Burhan ya ce: Har yanzu hanyar zaman lafiya da kawo karshen yakin a bude take, kuma duk wannan abu ne mai yiyuwa, kuma hanya a fili take, wato kungiyar RSF ta ajiye makamanta.

Ya tabbatar da cewa babu wata niyya ta tattaunawa da Rundunar ta RSF a yanzu, inda ya bayyana cewa kofar yin afuwa a bude take ga duk wanda ya ajiye makamansa. A ranar Asabar din da ta gabata ce sojojin kasar Sudan suka sake karbe ikon Kasuwar Libiya da ke yammacin birnin Omdurman, lamarin da ke nuna wani gagarumin mataki na ci gaba da suke samu, wanda ya biyo bayan sake kwac fadar shugaban kasa daga hannun dakarun RSF da sojojin na Sudan suka yi.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Gobe take Sallah a Nijeriya

An ga jinjirin watan Shawwal a Nijeriya da ke tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana.

Ɗaya daga cikin ’yan kwamitin duban wata a Nijeriya (NMSC), Malam Simwal Usman Jibrin ne ya sanar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.

Sai dai ya ce ana dakon sanar da ganin jinjirin watan a hukumance daga Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Islama a Nijeriya da ke ƙarƙashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi.

Hakan ya tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana, saboda haka gobe Lahadi take Sallah a Nijeriya.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • HOTUNA: Abba da Gwamnan Edo sun ziyarci iyalan mafarautan da aka kashe a Edo
  • Gwamna Abba Ya Nemi A Bayyana Fuskokin Waɗanda Suka Kashe ‘Yan Arewa A Edo
  • Iran Ta Ce Tattaunawa Da Amurka Tare Da Mai Shiga Tsakani Na Gaba, Ya Danganci Matakan Da Ta Dauka Kan Iran
  • Sarkin Gombe ya nemi manoma da makiyaya su zauna lafiya
  • Pezeshkian: Iran Ba Za Ta Yi Tattaunawa Kai Tsaye Da Amurka Ba
  • Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Legas, Mutane 10 Sun Kamu
  • Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Fiji: Ya Kamata A Koyi Fasahohin Da Kasar Sin Ta Samu A Fannin Raya Kasa
  • Gobe take Sallah a Nijeriya
  • An Tabbatar Da Ganin Watan Shawwal A Nijeriya