Aminiya:
2025-04-01@15:38:11 GMT

Matashi ya kashe jami’in tsaron Sarki Sanusi II a Kano

Published: 30th, March 2025 GMT

Rundunar ’Yan Sandan Kano, ta kama wani matashi bisa zargin kashe jami’in tsaron sa-kai a filin Idi yayin hawan sallah ƙarama.

A cewar sanarwar da ’yan sanda suka fitar, matashin mai shekara 20, ya daɓa wa jami’in wuƙa yayin da yake aiki tare da tawagar Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, bayan sallar Idi a ranar Lahadi.

Farashin fetur ya ƙaru sakamakon hana Dangote mai a Naira Babu tsamin dangantaka tsakaninmu da Gwamnan Sakkwato — Sarkin Musulmi

Haka kuma, wani jami’in sa-kai ma ya ji rauni kuma yana jinya a Asibitin Murtala Muhammad da ke Kano.

Rundunar ’yan sandan ta ce ta fara bincike kan lamarin, kuma ta gayyaci Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku, domin amsa tambayoyi.

A baya-bayan nan, ’yan sanda sun hana gudanar da Hawan Sallah a Kano, yayin da ake ci gaba da rikicin sarauta tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Hawan Sallah Sarkin Sanusi II

এছাড়াও পড়ুন:

HOTUNA: Abba da Gwamnan Edo sun ziyarci iyalan mafarautan da aka kashe a Edo

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da takwaransa na Jihar Edo Monday Okpebholo, sun ziyarci garin Torankawa da ke Kano domin jajanta wa iyalai da yan uwan mafarautan nan guda 16 da aka kashe a Jihar Edo.

Gwamnonin biyu sun ziyarci garin ne da manufar tabbatar wa da iyalan waɗanda lamarin ya shafa cewa lallai gwamnatin jihar Edo za ta hukunta waɗanda suka yi wannan aika-aika sannan kuma gwamnatin za ta biya su diyya.

Ta zuba wa abokan aikinta guba bayan taƙaddama kan ƙarin matsayi Mene ne matsayin azumin Sitta Shawwal a Mazhabar Malikiyya

“Wannan ziyara ba kawai ta jaje da ta’aziyya ba ce, a’a ta nuna tabbacin ƙoƙarin samar da adalci.

“Iyalan waɗannan mamata na buƙatar abin da ya fi kalaman baka — suna buƙatar aiwatar da duk abin da aka faɗa za a yi musu.

“Ba za mu zauna ba har sai mun ga an kama waɗanda suka yi wannan aika-aika, sai an yi holinsu a bainar jama’a sannan a hukunta su,” in ji Abba Kabir.

A nasa ɓangaren gwamnan jihar ta Edo, Monday Okpebholo ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan inda ya ba su tabbacin cewa gwamnatinsa za ta yi adalci ba daɗewa ba.

Aminiya ta ruwaito cewa, Abba ya buƙaci Sanata Okpebholo da ya tabbatar da biyan diyyar mafarauta da aka kashe a jiharsa ta Edo a hanyarsu ta komawa gida domin bukuwan Sallah.

Abba ya bayyana haka ne a lokacin da Gwamna Monday ya jagoranci tawagar gwamnatinsa zuwa Kano domin jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar bisa abin da ya faru na kisan matafiyan a makon jiya.

A jawabinsa, gwamna Abba ya yaba da ƙoƙarin takwaran nasa bisa matakan da ya ɗauka, inda ya ce a nasu ɓangaren sun ɗauki matakan da suka dace domin hana ramuwar gayya, “domin mutanen Kano masu son zaman lafiya ne da maraba da baƙi .

“Yawancin waɗanda aka kashe ɗin ’yan Kano ne. An tare su ne a jiharka a hanyarsu ta dawowa daga Fatakwal, aka gana musu azaba, sannan aka ƙone wasu daga cikinsu.”

Gwamna ya kuma yaba da ƙoƙarin gwamnatin Edo wajen ganin an ɗauko gawarwakin tare da binne su kamar addini ya tsara, da kuma kama wasu daga cikin waɗanda ake zargi.

Sai dai gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce yana da buƙatu biyu da yake so gwamnan ya yi ƙoƙarin ganin an cika su.

A cewasa, “muna so a gabatar da waɗanda ake zargi a gaban menama labarai domin duniya ta gansu kowa ya ga fuskokinsu. Wannan zai taimaka wajen kwantar da hankalin iyalan waɗanda aka kashe,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa Gwamnan na Edo ya faɗa cewa masa za a tabbatar da hukunci, “kuma ina da tabbacin gwamna zai cika wannan alƙawarin.”

Ya ce, “abu na biyu shi ne muna so a tabbatar da biyan diyyar waɗanda aka kashe ɗin ga iyalansu. Na san kai mutum ne mai nagarta da cika magana, kamar yadda ka ce za a biya diyya, muna so a biya diyyar cikakkiya, kuma a cikin lokaci.”

Tun da farko, gwamna Monday Okpebholo ya bayyana takaicinsa kan yadda lamarin ya faru, inda ya ce tuni an kama mutum 14 da ake zargi suna da hannu a lamarin kuma za su tabbatar da sun fuskanci hukunci.

Bayan wannan ganawar ce da ta gudana a Fadar Gwamnatin Kano, Gwamna Abba ya jagoranci Gwamna Okpebholo zuwa garin Torankawa da ke Karamar Hukumar Bunkure, domin jajanta wa iyalan waɗanda aka kashe.

Okpebholo ya shaida wa iyalan cewa ba zai yi ƙasa a gwiwa ba har sai an tabbatar da adalci.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • HOTUNA: Sarki Sanusi ya kai wa Abba ziyarar barka da Sallah
  • Sanusi II Ya Gudanar Da Hawan Nassarawa Duk Da Umarnin ‘Yansanda A Kano
  • HOTUNA: Sarki Sanusi ya kai wa Gwamna Abba ziyarar barka da Sallah
  • Muna kiran Natasha ta jingine gangamin da za ta yi a Kogi — ’Yan sanda
  • HOTUNA: Abba da Gwamnan Edo sun ziyarci iyalan mafarautan da aka kashe a Edo
  • Muna so a nuna wa duniya mutanen da suka kashe ’yan Arewa a Edo — Gwamnan Kano
  • Dan shekara 4 ya kira wa mahaifiyarsa ’yan sanda
  • Ƴansanda Sun Kama Wanda Ya Kashe Ɗan Bijilanti A Tawagar Sarki Sunusi II
  • Bayan Hukuncin ‘Yansanda, Sarki Sanusi II Ya Soke Hawan Sallah