Gwamna Umar Namadi Ya Taya Al’ummar Musulmi Murnar Bikin Sallah Karama
Published: 31st, March 2025 GMT
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya taya al’ummar Musulmi murna bisa kammala azumin watan Ramadan lafiya, tare da kira garesu da su rungumi koyarwar Annabi Muhammadu (S.A.W) a cikin rayuwarsu ta yau da kullum.
Ya bayyana hakan ne a sakon sa na Sallah ga al’ummar jihar.
Malam Umar Namadi ya yi addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da ya karɓi azumi da addu’o’in al’ummar Musulmi da suka yi a watan na Ramadan.
Haka kuma, ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da ya ci gaba da yi wa shugabanni jagorancin don yin abin da ya dace domin jin daɗin al’umma.
Namadi ya kuma yi addu’ar samun zaman lafiya, da hadin kai, da ci gaban tattalin arzikin ƙasa.
Radiyon Najeriya ya ruwaito cewa, Gwamnan ya kuma karɓi manyan baki da suka kai masa gaisuwar Sallah a Fadar Gwamnati da ke Dutse.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
DG VON Yayi Kira Ga Zaman Lafiya Da Hadin Kai Don Fadada Ci gaban Tattalin Arziki Da Ci Gaba.
Babban Darakta Muryar Najeriya VON, Malam Jibrin Baba Ndace ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kara kaimi wajen addu’o’in samun nasara ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a bisa tsarinta na sabunta fata.
Ya yi wannan kiran ne a cikin sakonsa na Sallah ga al’ummar Musulmi da aka rabawa manema labarai a Minna jihar Neja.
Malam Jibrin Baba Ndace ya tunatar da ’yan Najeriya cewa ya zama wajibi saboda nasarar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta samu ya kasance nasarar mu baki daya, don haka akwai bukatar mu kasance cikin nasara.
Daga nan sai ya mika gaisuwar ban girma ga daukacin al’ummar Musulmin Nijeriya da ma na duniya baki daya na bikin sallah karama tare da shawartar su da su dage wajen tallafa wa aikin Nijeriya domin samun sakamako mai ma’ana.
A cewarsa a madadin daukacin mahukunta da ma’aikatan gidan rediyon Muryar Najeriya, ina mika sakon gaisuwa da jinjina ga daukacin al’ummar musulmin Nijeriya da ma na duniya baki daya a daidai lokacin da muke gudanar da bukukuwan karamar Sallah mai albarka tare da shawartar su da su aiwatar da abin da suka koya a cikin azumin watan Ramadan.
Malam Jibrin Baba Ndace ya yi addu’ar Allah ya karawa ‘yan Najeriya farin ciki da walwala, da kuma sabon karfi domin su ci gaba da hada kai wajen samar da fahimtar juna, wajen bayar da gudunmawa mai kyau ga ci gaba da zaman lafiyar Nijeriya.
PR ALIYU LAWAL