Jiragen Yakin Amurka Sun Kai Sabbin Hare-Hare Kan Kasar Yemen A Daren Jiya
Published: 31st, March 2025 GMT
Jiragen yakin Amurka sun kai sabbin hare-hare kan kasar Yemen a daren Lahadi a wasu yankuna a birnin San’aa babban birnin kasar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bada sanarwan cewa a safiyar yau Litinin ne jiragen yakin Amurkan suka kai hare-hare har 13 a kan wurare daban-daban a kasar, daga ciki har da Yankunan Malikah da Sarf na birnin San’aa babban birnin kasar.
Wasu kafafen yada labaran kasar Yemen sun bayyana cewa, kafin haka jiragen yakin Amurka sun kai hare-hare a kan kasar ta Yemen wadanda suka kai ga shahadar fararen hula 12 da kuma raunata wasu 2 a birnin San’aa babban birnin kasar.
Washington ta bada sanarwan cewa ta na kai hare-haren don tabbatar da tsaron jiragen ruwan kasuwanci da suke wucewa a tekun red Sea. Alhali gwamnatin kasar Yemen ta ce tana kai hare-hare kan jiragen ruwan HKI ko masu zuwa HKI ne kawai. Sauran jiragen ruwan kasuwanci suna wucewa ba tare da wata matsala ba.
Banda haka sojojin kasar Yemen sun maida martanin hare-haren da Amurka take kaiwa kan kasar, tare da cilla makamai masu linzami kan jiragen yakin Amurka da na HKI a tekun re sea da kuma tashar jiragen sama ta Bengerion a HKI.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: jiragen yakin Amurka kai hare hare kasar Yemen
এছাড়াও পড়ুন:
An Gayyaci Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Abbas Aragchi Taron Makamashin Nukliya A Amurka
Bayan taro na biyu tsakanin JMI da Amurka a birnin Roma na kasar Italiya a jiya Asabar an gayyaci ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arachi don gabatar da Jawabi a wani taro wanda mahukuntan kasar Amurka suka shirya.
Kamfanin dillancin labarai IP na kasar ya nakalto masu shirya taron na cewa an gayyace Abbas Arichi don gabatar da jawabin ne don muhuntan Amurka su ji ta bakin wadanda suka kore a sanin amfanin makamashin nukliya ta zaman lafiya da kuma tattaunawa a kansa.
Labarin ya nakalto wadanda suke gudanar da taron wato ” The Carnegie International Nuclear Policy Conference” wanda za’a fara a gobe litinin, na cewa taron yana taimakawa mahukuntan kasar Amurka sanin kan yadda jami’an diblomasiyya yakamata su fahinci abubuwan da suke da sarkakiya a cikin fasahar nukliya.
Har’ila yau ana son jin yadda Iran take gudanar da shirin ta makamacin Nukliya ta zaman lafiya a duk tsawon shekarun da suka gabata.
Labarin ya kara da cewa mai yuwa ministan ya halarci taron ta hotunan bidiyo daga nan Tehran. Labarin ya kammala da cewa taron Amurka da Iran dangane da shirinta na makamashin Nukliya da aka kammala a birnin Ruma ne ya tada wannan bukatar ta jin bangaren Iran dangane da fannonin da ake sarrafa makamashin nukliya ta zaman lafiya.