Aminiya:
2025-04-22@04:14:59 GMT

Dan shekara 4 ya kira wa mahaifiyarsa ’yan sanda

Published: 31st, March 2025 GMT

Wani yaro dan shekara hudu da ya kira wayar salular ’yan sandan yankin Mount Pleasant a Karamar Hukumar Charleston Jihar South Carolina da ke Amurka ya ce, mahaifiyarsa ta shanye masa ‘ice cream’ dinsa kuma yana bukatar a hukunta ta, a kai ta gidan yari saboda aikata hakan.

A cewar ’yan sanda yaron dan shekara 4 ya yi kururuwa, inda ya kira ’yan sanda bayan mahaifiyarsa ta shanye masa ice cream dinsa.

Sarkin Gombe ya nemi manoma da makiyaya su zauna lafiya Matashi ya kashe jami’in tsaron Sarki Sanusi II a Kano

Al’amarin ya faru ne a cikin a garin Mount Pleasant, Wisconsin — mai nisan kilomita bakwai, yamma da Racine — lokacin da yaro dan shekara 4 ya tuntubi ‘yan sanda, inda ya ce, mahaifiyarsa ba ta kyauta masa ba, a cewar wata sanarwa da ’yan sandan kauyen Mount Pleasant suka fitar.

“An aika jami’an ’yan sanda, wato Gardinier da Ostergaard don amsa kiran mai korafin neman agajin jami’an 911, wanda ya bayyana cewa, mahaifiyarsa ba ta kyauta masa kuma yana bukatar a kai ta gidan yari”, in ji hukumomi.

Lokacin da jami’ai suka isa gidansu, yaron ya ce, mahaifiyarsa ta shanye masa ‘ice cream’ dinsa kuma yana bukatar a ka ita gidan yari saboda aikata hakan.

Daga bisani ya kuma shaida wa ’yan sanda cewa, ba ya son a kai mahaifiyarsa gidan yari kawai, yana son a biya shi ‘icecream’ da ta shanye masa.

Daga baya jami’an sun bar gidan bayan sun gano cewa, wannan shi ne dalilin da ya sa aka kira su, amma sun dawo washegari, wanda a wannan karon suka ba wa yaron mamaki, inda suka kawo masa ice cream, “bayan ya yanke shawarar cewa ba ya son mahaifiyarsa ta shiga matsala,” in ji ’yan sanda.

Jami’an ’yan sandan da suka amsa kiran, ba su kaɗai ne suka gano abin dariya game da lamarin ba.

“Ban ce yana da gaskiya ba. Abin da nake fada shi ne na fahimta,” in ji wani mutum da ke mayar da martani ga ofishin ’yan sanda na kauyen Mount Pleasant game da lamarin a shafukan sada zumunta na zamani.

“Aƙalla ya san yadda ake kiran lambar taimako ko neman agajin jami’an tsaro,” in ji wata. “Zai iya ceton ran wani wata rana!”

Jami’an ’yan sandan da suka ziyarci gidan su yaron sun dauki hoto tare da yaron mai shekara 4 bayan an warware matsalar, inda suka samu damar yin barkwanci.

“Ina son jin labarin jami’anmu game da abin ban mamaki, inda suke samar da kyakkyawar dangantaka tsakaninsu da yara,” in ji wani mai amfani da kafofin sada zumunta.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda yaro mahaifiyarsa ta

এছাড়াও পড়ুন:

Hyda Ghaddar: Mai Son Horar Da ‘Yanmatan Kano Kwallon Kafa

Hyda ta bude kungiyar kwallon kafa ta ‘Breakthrough Football Academy’ a Kano watanni shida da suka gabata inda take da burin bai wa Kanawa dama su shiga duniyar wasanni inda a hirarta ta sashin Hausa na BBC ta ce ta zama kociya ce saboda tunanin da take da shi na taimakon al’ummar Kano bisa la’akari da irin taimakon da al’ummar Kano suka yi mata itama.

Ta ce “Babban burina shi ne samun wasu daga cikin wadanda nake bai wa horo sun yi fice a duniyar kwallo.” Ta kuma kara da cewa wani karin burin nata shi ne a samu babbar kungiyar wasa ta mata zalla a Kano “Domin a Kano akwai matan da suka iya kwallon kafa amma saboda rashin dama ba a jin su.”

Kungiyar tata mai suna ‘Breakthrough Football Academy’ na gayyato ‘yan wasa kuma “idan sun ga mutum ya yi musu sai su rike shi idan kuma bai dace ba sai su ba shi hakuri. Hyda Ahmad Ghaddar ta yi wasan kwallon kafa inda kuma ta fi taka ‘yar wasan tsakiya sannan ta ce ta samu kwarin gwiwa daga iyalinta tun daga farko kasancewarsu masu son kwallon kafa ne.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Abubuwan da suka sa Fafaroma Francis ya yi fice a duniya
  • Miji ya yi wa matarsa saki 3 a ofishin ’yan sanda
  • Fadar Vatican Ta Sanar Da Mutuwar Paparoma Francis A Safiyar Yau Litinin
  • Yadda ma’aikatan gidan ruwa 4 suka mutu a Bauchi
  • Bikin Easter : Paparoma Francis ya yi kira da a tsagaita wuta a Gaza
  • Fursunoni 9 Sun Tsere Daga Gidan Gyara Hali A Jihar Kwara, An Cafko Guda Daya
  • Hyda Ghaddar: Mai Son Horar Da ‘Yanmatan Kano Kwallon Kafa
  • ’Yan sanda sun ceto ɗalibai 10 sun kashe ɗan bindiga a Edo
  • An buɗe wa jami’an NDLEA wuta a Abuja
  • ’Yan sanda sun ceto ɗalibai 10 sun lashe ɗan bindiga a Edo