Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci: Kasashen Yamma Sune Yan Ta’adda Na Gasliya A Yankin
Published: 31st, March 2025 GMT
Watan Ramadan mai alfarma na wannan shekara ya zo ni’imomi masu Yawa wanda matasa da sauran mutanen kasa sun amfani da ayyukan ibada wadanda suka hada da karatun Alkur’ani mai girma, mun yi addu’o’I mun kuma yi magana da All..mun roke shi a cikin watan. Da fatan All..ya karbi ayyukammu.
Amma a wani bangare a cikin wannan Ramadan, duk tare da jin dadin da muka samu, amma watan yana tattare da dacinsa, kissan mutanen Falasdinu, tare da goyon bayan Amurka.
Kasashen yamma suna tuhumar Iran tana amfani da sojojin wadanda suke wakiltantan a abinda yake faruwa a yankin. Amma gaskiyar al-amarin sune suke da wakili a wannan yakin, kuma itace HKI, wacce taek wakiltansu a ayyukan ta’addanci da take yi a kasashen Falasdinu, Siriya da sauransu.
Idan Falasdinawa sun tashi suna kare kasarsu sai su ce ai yan ta’adda, alhali sune yan ta’adda na gaskiya.
Ayyukan HKI a yankin sun hada da kashe masana a cikin gaza, Iraki , Lebanon iran da sauransu suna kashesu.
Muna ganin yadda matasa a kasashen yamma suke fitowa kan tunia suna nuna rashin amincewarsu da abinda kasashen yamma tare da amfani da HKI suke yi a Gaza, wannan ya nuna basu san abinda yake faruwa tun da dadewa da sun san fiye da haka da zasu kara tashin kan gwamnatocinsu.
Idan sun yi kokarin tada fitana a cikin gida mutanen kasar iran da kansu zasu bada amsa a kan irin wadannan fitinu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kakakin Ma’aikatar Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Babban Abin Da Suke Bukata Shi Ne Daga Takunkumi
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Babban abin da suke bukata a duk wata tattaunawa shi ne a dage takunkumi
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Isma’il Baqa’i, ya jaddada cewa babban bukatar Iran a duk wata tattaunawa ita ce a dage takunkumin da aka kakaba mata ta hanyar da za ta kai ga samun sakamako mai ma’ana.
Isma’il Baqa’i ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai na mako-mako da yake yi a yau litinin cewa: A kwanakin baya ministan harkokin wajen kasar Iran ya ziyarci kasar Rasha, sannan ya gana da ministan harkokin wajen kasar Italiya, a gefen shawarwari ba na kai tsaye ba tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Amurka.
Ya kara da cewa: A gobe ne ministan harkokin wajen kasar Iran zai kai ziyarar aiki zuwa kasar China. Ya kuma kara da cewa, ana ci gaba da samun wasu ci gaba a daidai wadannan ziyarce-ziyarcen, yana mai jaddada cewa idan aka yi tambayoyi a kansu a yayin taron tambayoyi da amsa, zai ba da cikakkun bayanai.