Aminiya:
2025-04-01@23:30:32 GMT

Nijar ta fice daga rundunar MNJTF mai yaƙi da masu iƙirarin jihadi

Published: 31st, March 2025 GMT

Nijar ta fice daga rundunar tsaro ta haɗin gwiwa da ke yaƙi da masu iƙirarin jihadi a Tafkin Chadi da ke yammacin Afirka yayin da take ƙoƙarin inganta tsaro kan albarkatun mai a cikin gida.

A shekarar 2015 ce Nijeriya da Chadi da Kamaru da Nijar suka sake farfaɗo da rundunar haɗin gwiwa ta Multinational Joint Task Force (MNJTF), wacce aka ƙirƙira a shekarar 1994 don yaƙi da ƙungiyoyin jihadi a kewayen Tafkin Chadi.

NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Komawa Cin Abinci Yadda Ya Kamata Bayan Watan Ramadana Azumin Sitta Shawwal a Musulunci

Sai dai har yanzu ana ci gaba samun rarrabuwar kai da matsalar rashin daidaito na hana rundunar samun nasara sosai, lamarin da ya sa ƙungiyoyin ‘yan bindiga a yankin cin karensu ba babbaka.

Kamfanin Dillancin Labaran Reuters da ya ruwaito sanarwar gwamnatin ƙasar Nijar ɗin ya ce kawo yanzu MNJTF ba ta yi tsokaci game da ficewar Nijar ɗin ba, yana mai ƙarawa da cewa babu tabbas game da yadda matakin zai yi tasiri kan aikin rundunar a nan gaba.

Yankin Tafkin Chadi yana fama da hare-haren ‘yan bindiga ciki har da ‘yan kungiyar ISWAP da Boko Haram, waɗanda suka ƙaddamar da yaƙi a arewa maso gabashin Nijeriya a shekarar 2009 kuma sun kashe dubban mutane.

A bara, Chadi ta yi barazanar ficewa daga MNJTF bayan an kashe sojojinta kusan 40 a wani harin da aka kai wani sansanin soji.

Nijar tana rage hulɗa da wasu maƙwabtanta tun bayan da sojoji suka hamɓarar da gwamantin Shugaba Mohamed Bazoum a shekarar 2023. Tare da Burkina Faso da Mali – ƙasashe maƙwabta, inda sojoji suka karɓe kwanan nan – ta janye daga ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS) a shekarar 2024.

Sojojin da ke mulki a Nijar, da suka yi shelar tsarin miƙa mulki na shekara biyar, sun yi alƙawarin tabbatar da tsaro a ƙasar, wadda ‘yan ci-rani da masu safarar mutane ke ƙetarewa ta cikin gagarumar hamadar arewacinta.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Boko Haram ISWAP Nijar

এছাড়াও পড়ুন:

Sarkin Gombe ya nemi manoma da makiyaya su zauna lafiya

A Bikin Yawan Sallah na Jafi da aka yi a fadar Sarkin Gombe, Mai Martaba Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III, ya yi kira ga manoma da makiyaya da su zauna lafiya da juna.

Sarkin ya ce zaman lafiya shi ne ginshiƙin ci gaba, kuma haɗin kai tsakanin manoma da makiyaya zai hana rikice-rikice da ke barazana ga jihar.

Matashi ya kashe jami’in tsaron Sarki Sanusi II a Kano Gwarzon gasar Alƙur’ani ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga a Katsina

“Ina roƙon manoma da makiyaya da su zauna lafiya don guje wa rigingimu.

“Kowa yana da haƙƙin tabbatar da zaman lafiya domin hakan na kawo ci gaban tattalin arziƙi da walwalar al’umma,” in ji Sarkin.

Haka kuma, ya tabbatar da cewa masarautar Gombe za ta ci gaba da goyon bayan gwamnatin jihar domin tabbatar da tsaro mai ɗorewa.

Sarkin ya gode wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa ƙoƙarinsa na inganta rayuwar al’umma da ɗaukar matakan tsaro, musamman samar da motocin aiki ga jami’an tsaro.

Bikin hawan sallah na Jafi ya samu halartar manyan baƙi, ciki har da Gwamnan Jihar Gombe da wasu manyan jami’an gwamnati, inda aka jaddada buƙatar haɗin kai da zaman lafiya a jihar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tsohon Gwamnan Zamfara Ya Bukaci A Ci Gaba Da Tallafawa Mabukata Bayan Ramadan.
  • Sanata Yari Zai Tallafa Wa Marayu 20,000 A Zamfara
  • Nijar Ta Fice Daga Rundunar Tsaro Ta Haɗin Kai MNJTF
  • Kisan Mafarauta: Matakan da gwamnatin Edo da ta Kano suke ɗauka
  • Sarkin Gombe ya nemi manoma da makiyaya su zauna lafiya
  • Eid-el-Fitr: Sarkin Kauru Ya Gargadi Masu Bai Wa ‘Yan Ta’adda Bayanai
  • Matashi ya kashe jami’in tsaron Sarki Sanusi II a Kano
  • Gwarzon gasar Alƙur’ani ya Kuɓuta daga hannun ’yan bindiga a Katsina
  • An Gudanar Da Gagarumar Zanga- Zanga Ta Ranar Qudus Ta Duniya A Birnin Roma Na Kasar Italiya