A Yau Litinin Ce Aka Gudanar Da Sallar Edi Da Bukukuwan Sallah A Nan Iran Da Wasu Kasashen Musulmi
Published: 31st, March 2025 GMT
A safiyar yau litinin ce a nan Iran da kuma wasu kasashen duniya da dama suka gudanar da sallar Idi wanda ya kawo karshen watan Ramadan mai al-farma wanda musulmi suka yi azuminsa daga safe zuwa faduwar rana na tsawon kwanaki 29-ko 30.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa a nan Tehran dubban daruruwan mutanen suka fito zuwa babbar masallacin Imam Khumaini dake tsakiyar birnin Tehran inda suka gudanar da sallah mai raka’o’I biyu tare da jagorancin Jagoran juyin juya halin musulunci a kasar Imam Sayyid Aliyul Khamina’e.
Duk da cewa ana samun babbanci tsakanin musulmi kan ranar ajiye azumun amma akalla ba wanda zai yi azami kasa da kwanaki 29.
A cikin watan dai, musulmi sukan yawaita karatun alkur\ani mai girma da kuma kokarin sanin ma’anarsa da kuma zrfafa tunani a cikinsa.
Har’ila yau watan ne na yawaita sadaka na abinci da kuma duk abinda zai taimakawa masu karamin karfi a tattalin arziki.
Musulmi sukan yawaita addu’a da neman gafarar All..a kan zunubban da suka aiakata sannan suna yawaita salloli.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasashen Iran Da Tunisya Suna Shirin Bunkasa Alaka A Fagagen Yawon Bude Ido
Minista mai kula da al’ada da yawon bude ido da kuma sana’o’in hannu na Iran Ridha Salihi wanda ya gana da jakadan Tunisiya a Iran,Imad al-Rahmani ya bayyana bukatar hanyoyin bunkasa alakar yawon bude ido a tsakanin kasashen biyu, yana mai kara da cewa: Yarjejeniyar da aka cimmawa a tsakanin kasashen biyu dangane da yawon bude ido wani yunkuri ne mai matukar muhimmaanci.
Kamfanin dillancin labarum “Iran” ya ambato; Ridha Salihi Amiri yana mai yin ishara da tarihin alakar kasashen biyu ta fuskar al’adu, sannan ya kara da cewa; Kasar Tunis ta samu ci gaba sosai a tsakanin kasashen Lrabawa ta fuskar inganta harkokin yawon bude ido. Haka nan kuma ya yi ishara da yadda Iran take da wuraren bude ido mabanbanta da su ka hada da na tarihi da kuma na dabi’a, sannan ya kara da cewa: Iran din tana da cibiyoyi na karbar bakuncin masu zuwa yawon bude ido.
A nashi gefen, Imad al-Rahmani ya bayyana muhimmancin alakar dake tsakanin kasashen biyu yana mai kara da cewa: “Tarayyar da kasashen biyu su ka yi a cikin al’adu za su iya share fage na yin aiki tare mai dorewa, kuma sama da zirga-zirgar jiragen sama a tsakanin kasashen biyu kai tsaye za ta taimaka wajen bunkasa wannan alakar.