Aminiya:
2025-04-02@01:51:35 GMT

Kisan Mafarauta: Matakan da gwamnatin Edo da ta Kano suke ɗauka

Published: 31st, March 2025 GMT

Har yanzu dai kisan wasu matafiya ’yan Arewa da aka yi a garin Uromi da ke Ƙaramar Hukumar Arewa maso Gabashin Esan na ci gaba da tayar da ƙura a faɗin Nijeriya.

A bayan nan ne wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta suka nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga Kudanci zuwa Arewacin Nijeriya.

Hotunan bidiyon sun nuna yadda aka yi wa waɗanda abin ya shafa jina-jina sannan aka cinna musu wuta suka ƙone ƙurmus.

Za mu tura tawaga ƙauyen Torankawa —Gwamnatin Kano

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa zai tura tawaga ta musamman zuwa ƙauyen Torankawa domin jajanta wa iyalan mafarautan da aka kashe a Jihar Edo.

Hakan dai na ƙunshe ne cikin saƙonsa na barka da sallah kamar yadda mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a jiya Lahadi.

Wasu majiyoyi daga fadar Gwamnatin Kano ta ce ana kuma sa ran karɓar baƙuncin Gwamnan Edo domin jajanta wa gwamnatin da kuma iyalan waɗanda lamarin ya shafa.

Al’ummar Edo a Kano sun yi Allah wadai da lamarin

Ƙungiyar mazauna Edo da ke Jihar Kano ta yi tir da faruwar lamarin, tana mai neman da a bi wa waɗanda lamarin ya shafa haƙƙinsu.

Wata sanarwa da mai magana da yawun ƙungiyar , Mista Philip Tomon ya fitar, ya jajanta wa iyalan mafarautan da aka yi wa kisan gillar yana mai kiran mahukunta da su tabbatar an yi adalci a lamarin.

Ƙungiyar Mafarauta ta jingine zanga-zanga

A wata sanarwa da Sakataren Ƙungiyar Mafarautan Kano, Usman Mu’azu Abdullahi Yakasai ya fitar, ya ce sun jingine zanga-zangar da suka shirya gudanarwa.

Sai dai sakataren wanda aka fi sani da Alaska duk da tana cikin alhini ta jingine zanga-zangar ce bayan tuntuɓe-tuntuɓen da ta yi, inda ta miƙa wa Gwamnatin Kano ƙorafi a hukumance na neman yi wa waɗanda aka kashe adalci.

Alaska ya ce ƙungiyar ta gamsu da irin matakan da ake ɗauka wajen tunkarar lamarin, kuma tana fatan doka za ta yi aiki yadda ya kamata.

Gwmanan Edo a Najeriya, Monday Okpebholo, ya dakatar da Kwamandan Rundunar Samar da Tsaro a jihar Friday Ibadin, biyo bayan kisan da aka yi wa mafarauta 16 ƴan asalin yankin arewacin kasar a alhamis da ta gabata.

SWannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Umar Musa Ikhilor ya fitar mai cewa an ɗauki matakin ne la’akari da bayanan da ke ƙunshe a rahoton binciken farko da aka gudanar dangane da wannan lamari, wanda ya yi matuƙar girgiza jama’a a Najeriya.

‘’ Lura da abubuwan da suka faru a ranar ta 27 ga watan Maris na 2025 a garin Uromi na ƙaramar hukumar Esan, inda aka samu asarar rayukan wasu matafiya, Mai Girma gwamna Monday Okpebholo, ya bayar da umurnin dakatar CP mai ritaye Friday Ibadin, Kwamandan Rundunar Samar da Tsaro ta jihar daga matsayinsa,’’ a cewar sanawar.

An rusa duk ƙungiyoyin ’yan bangar da ba su da rajista

Har ila yau, sanarwar da Sakataren Gwamnatin jihar ta Edo ya fitar ta ƙara da cewa an rusa ilahirin ƙungiyoyin ’yan banga da ba su da rajista a jihar, biyo bayan wannan kisa.

Sanarwar ta ci gaba da cewa ’yan bangar da suka aikata wannan ta’asa, suna aiki ne ƙarƙashin inuwar wata ƙungiya da ba ta da rajista, saboda haka ya zaman wajibi a ɗauki wannan mataki don tabbatar da samar da yanayi na tsaro a jihar.

Mahukuntan Edo na tattaunawa da takwarorinsu na Kano kan lamarin

Yanzu haka ana ci gaba da bincike dangane da wannan lamari, kuma tuni aka kama mutane 14 da ake zargi, yayin da ake farauta wasu mutane da dana da suka arce kamar dai yadda Babban Sufeton ’yan sandan Nijeriya ya bayar da umarni.

Gwamnatin Edo ta ce tana ci gaba da tattaunawa da dangin marigayan, da kuma mahukuntan jihar Kano, lura da cewa mafi yawan ’yan asalin jihar ne, tare da ɗaukar alƙawarin cewa za a tabbatar da adalci ta hanyar hukunta waɗanda aka sama da laifi.

Bayanan da suka fito fili bayan faruwar wannan lamari, sun tabbatar da cewa mafarautan sun fito ne daga Fatakwal da ke Jihar Ribas a hanyarsu ta zuwa Kano domin yin bukukuwan sallah a cikin iyalansu.

Ya zama dole a hukunta masu laifi a lamarin — CAN

Ƙungiyar Kiristoci a Najeriya (CAN) ta yi tir da Allah wadai dangane da kisan da aka yi wa mafarauta 16 a lokacin da suke ratsa jihar Edo a hanyarsu ta komawa a arewacin ƙasar.

A sanarwar da ta fitar ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar Archbishop Daniel Okoh a ranar Lahadi, da farko CAN ta isar da saƙon nuna alhini zuwa ga ƴan uwa da aminan waɗanda suka rasa rayukansu, daga nan kuma ta yi kira ga mahukunta da su ɗauki matakan da suka wajaba domin tabbatar da cewa ana aiki da doka da kuma cusa wa jama’a ra’ayin yarda da tsarin shari’a na ƙasar.

Daga nan sai sanarwar ta ce ‘’alhaki ya rataya a wuyan gwamnati domin tabbatar da cewa an gudanar da bincike da nufin hukunta waɗanda ke da hannu a wannan lamari da za a iya bayyana shi a matsayin mummunan cin zarafin bil Adama’’.

Har ila Ƙungiyar ta Kiristocin Najeriya ta isar da saƙon taya murna ga al’ummar Musulmi dangane da bukukuwan sallar da suke yi bayan sun kammala azumin watan Ramadan.

Ƙungiyar Amnesty International mai fafatikar kare haƙƙin ɗan Adam ta ce dole binciken da za a yi, ya zama sanadiyar hukunta waɗanda suke da hannu a kisa tare da ƙona matafiya ’yan arewa da aka yi a garin Uromi da ke Jihar Edo.

Shugaban ƙungiyar a Nijeriya, Isa Sanusi ne ya bayyana haka, inda, “dole hukumomin Najeriya su tabbatar an gudanar da bincike a bayyane, sannan kuma binciken ya zama silar adalci ga waɗanda aka kashe da iyalansu.

“Ya kamata a riƙa bayyana yadda binciken ke gudana tun daga farko har zuwa lokacin yanke hukunci.”

Amnesty ta ce abin da ya faru Uromi na nuna yadda ake ƙara samun ƙungiyar ’yan sa-kai na garuruwan da suke kusa da manyan hanyoyi suke tare hanyoyin suna aikata ba daidai ba.

“Yadda aka daɗe ana irin waɗannan kashe-kashen na nuna akwai gazawar gwamnati wajen kare rayukan al’ummarta.”

Isa Sanusi ya ƙara da cewa Amnesty ta yi Allah wadai da kisan, sannan ya sake nanata kiransu ga gwamnatin Najeriya da ta ɗauki matakin da ya dace.

Dole a kawo ƙarshen kisan gillar da ake yi wa ’yan Arewa

Ƙungiyar dattawan arewa ta magantu kan kisan matafiya ƴan yankin arewa da aka yi a garin Uromi da ke jihar Edo, inda ta ce yankin arewa ya daɗe yana haƙuri da cin kashin da ake yi masa, amma kuma an kusa ƙure su.

Ƙungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da kakakinta, Farfesa Abubakar Jika Jiddere ya fitar.

Sanarwar ta ce, “dattawan arewa sun damu matuƙa da kisan dabbanci da rashin tausayi da aka yi wasu mafarauta ƴan arewa da suke hanyarsu ta komawa gida arewa domin bikin sallah. Muna Allah wadai da wannan aika-aikar.

“Mun daɗe muna haƙuri da irin wannan cin kashin da ake mana a kudancin Nijeriya. Dole a kawo ƙarshensa haka,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa dole a kama waɗanda suka aikata laifin, sannan a musu hukunci a bayyane.

“Sannan dole a biya diyyar waɗanda aka kashe kamar yadda yake a addinance, sannan dole gwamnatin Edo ta fito ta bayar da haƙuri.”

Dattawan sun kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta Edo ta cika waɗannan buƙatun nan da kwana da 14, “idan kuma ba a ga wani mataki ba zuwa lokacin, dattawan arewa za su yi amfani da duk matakan da suka dace wajen bin haƙƙin ƴaƴanta da aka kashe.”

A bi mana haƙƙi — ’Yan uwa

Wakilan Aminiya sun ziyarci ƙauyen Torankawa da ke Ƙaramar Hukumar Bunkure a Jihar Kano, inda suka zanta da wasu daga cikin iyalan mafarautan da aka kashe.

Wasu daga cikin iyalan mafarautan kuma mazauna ne a ƙauyukan ƙananan hukumomin Garko, Kibiya da Rano da ke Jihar Kanon.

Tun dai bayan samun labarin faruwar lamarin ne mazauna ƙauyen Torankawa da aka sansu da sana’ar farauta suka shiga cikin alhinin da suka ce ba su taɓa faɗawa makamancinsa ba.

Shida daga cikin mafarautan da aka kashe da wani ɗaya da ya tsallake rijiya da baya sun fito ne daga ƙauyen.

Daga cikin mamatan akwai Abdulkadir Umar, wanda ya rasu ya bar mata biyu da mahaifiyarsa.

Sai kuma Zahraddeen Tanko wanda ya bar mata ɗaya da ’ya’ya huɗu da kuma Haruna Hamidan wanda shi ma ya rasu ya bar mata ɗaya da ’ya’ya huɗu.

Akwai kuma Usaini Musa wanda ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya biyu da Abdullahi Harisu wanda ya yi aure watanni huɗu da suka gabata da kuma Ya’u Umaru da Abubakar Ado da ba su kai ga yin auren ba ma.

Duk ’yan uwan mamatan da Aminiya ta zanta da su sun bayyana alhini — wasunsu cikin hawaye suna roƙon mahukunta da su bi musu haƙƙinsu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jihar Edo Jihar Kano mafarauta Monday Okpebolo mafarautan da aka ƙauyen Torankawa iyalan mafarautan wata sanarwa da Allah wadai da wannan lamari a garin Uromi waɗanda aka da aka yi wa da ke jihar da ke Jihar ya bar mata tabbatar da

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Edo Okpebholor Ya Jajantawa Iyalan Wadanda Aka Kashe

Game da aka yi wa mafarauta 16 a Udune Efandion, karamar hukumar Uromi ta jihar Edo, gwamna Monday Okpebholo ya yi kakkausar suka ga wannan aika-aika na rashin hankali, yana mai bayyana hakan a matsayin “wani abu da kuma muguwar dabi’a.

 

 

Okpebholo, tare da Gwamna Abdullahi Yusuf na Jihar Kano, sun yi addu’a ga rayukan wadanda abin ya shafa a kauyen Bunkure na jihar Kano inda wadanda abin ya shafa suka fita tare da kuma da bada tabbacin ga iyalan wadanda abin ya shafa cewa za a gurfanar da masu laifin gaban kuliya.

 

Allah wadai da gwamnan ya biyo bayan harin da wasu gungun ’yan bindiga suka kai wa mafarautan, wadanda aka yi kuskuren cewa masu garkuwa da mutane ne, wanda ya yi sanadin kashe mutane 16.

 

 

Lamarin dai ya janyo cece-ku-ce, inda shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin a farauto wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da umurtar jami’an tsaro da su gudanar da bincike cikin gaggawa.

 

Okpebholo ya bada tabbacin cewa gwamnatin sa za ta dauki dukkan matakan da suka dace domin ganin an kamo duk wanda ke da hannu a harin tare da gurfanar da shi gaban kuliya. Ya zuwa yanzu dai an kama mutane 14 da ake zargi da hannu a lamarin.

 

Gwamnan ya kuma yabawa al’ummar jihar Kano da ma daukacin yankin Arewa kan rashin daukar doka a hannunsu da sunan harin ramuwar gayya.

 

 

Ya sanar da cewa, ana shirin bayar da diyya ga duk wadanda lamarin ya shafa.

 

Gwamna Yusuf wanda ya karbi bakuncin Okpebolo a Kano, ya yi alkawarin bayar da tallafin kudi da kayan abinci ga iyalan mafarauta da aka kashe a Uromi, jihar Edo.

 

 

Ya kuma yi alkawarin cewa za a biya diyya ga wadanda lamarin ya shafa, yana mai jaddada cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa.

 

 

ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Edo Za Ta Biya Diyyar Mafarauta ‘Yan Kano 16 Da Aka Kashe A Uromi 
  • HOTUNA: Abba da Gwamnan Edo sun ziyarci iyalan mafarautan da aka kashe a Edo
  • Gwamna Edo Okpebholor Ya Jajantawa Iyalan Wadanda Aka Kashe
  • Gwamna Abba Ya Nemi A Bayyana Fuskokin Waɗanda Suka Kashe ‘Yan Arewa A Edo
  • Muna so a nuna wa duniya mutanen da suka kashe ’yan Arewa a Edo — Gwamnan Kano
  • Gwamnan Edo Ya Ziyarci Sanata Barau Kan Kisan Yan Arewa 16
  • YANZU-YANZU: Gwamnan Edo Ya Kai Ziyarar Jaje Kan Kisan Mafarauta A Uromi
  • Iran Ta Ce Tattaunawa Da Amurka Tare Da Mai Shiga Tsakani Na Gaba, Ya Danganci Matakan Da Ta Dauka Kan Iran
  • Kashe Matafiya: Gwamnatin Kano Ta Aika Tawaga Zuwa Edo