Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya bayyana rashin jin daɗinsa dangane da kashe matafiya ’yan Arewa da aka yi a Jihar Edo.

Saboda haka Sarkin ya ce suna dakon ganin hukuncin da za a ɗauka dangane da faruwar wannan mummunan lamari.

Kisan Mafarauta: Matakan da gwamnatin Edo da ta Kano suke ɗauka Dalilin da muka soke Hawan Bariki — Masarautar Zazzau

Da yake miƙa saƙon gaisuwar Sallah ga Gwamnan Sakkwato, Alhaji Ahmad Aliyu a ranar Litinin, Sarkin ya ce “mun ga an ɗauki mataki kan yanayin da ake ciki a Jihar Edo.

“Saboda haka muna jiran ganin hukuncin da za a ɗauka bayan kammala bincike don ba wani dalili ka kashe mutum ba tare da wani haƙƙi ba.

“Muna kiran jami’an tsaro da su tashi tsaye domin tabbatar da cewa jama’a ba su fusata ba sun ɗauki hukunci a hannunsu.

“Idan a wani wurin mutanen banza sun ɗauki hukunci a hannunsu, mu a nan Sakkwato ba za mu bari a yi abin da bai kamata ba.

“Mu sanya ’yan uwanmu da abin ya faru da su a cikin addu’a sannan muna kiran gwamnati da jami’an tsaro su ɗauki matakin kare rayukkan jama’a,” a cewar Sarkin Musulmi.

Sarkin ya ƙara da cewa “bai kamata a riƙa yaɗa abin da bai dace ba a kafafen sadarwa na zamani da za su janyo tashin hankali a wurin da ake da zaman lafiya.

“Duk wani abu da ya faru a wani wuri, bai kamata wasu da ke can wani wurin na daban su ce za su ɗauki mataki a Sakkwato ko Kano ko Kaduna kan wani abun da ya faru a Jihar Edo ko Legas ba.”

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jihar Kano mafarauta Yan Arewa

এছাড়াও পড়ুন:

Somalia: Harin Amurka a kan kungiyar IS ya kashe wasu mambobin kungiyar

Rundunar sojin Amurka ta kaddamar da wani hari ta sama a ranar Asabar din da ta gabata kan mayakan IS a yankin Puntland na Somalia, inda suka kashe wasu mambobin kungiyar da dama, a cewar rundunar sojin Amurka .

A cikin wata sanarwa da ta fitar, rundunar sojin Amurka da ke nahiyar Turai ta tabbatar da cewa, harin da aka kai tare da hadin gwiwar gwamnatin Somaliya, ya kashe da dama na mayakan ISIS a Somaliya.

Yayin da kungiyar IS ke hankoro hada karfinta a Somalia  wanda bai bunkasa ba idan aka kwatanta da kungiyar Al-Shabaab mai alaka da Al-Qaeda, kungiyar ta mayar da hankalinta ne wajen kara fadada karfinta a yankin Puntland mai cin gashin kansa.

“Harin ya auke ne a kudu maso gabashin Bosasso, Puntland, a arewa maso gabashin Somalia,” in ji sanarwar.

Wannan farmakin ya biyo bayan wani harin makamancin haka ne kwanaki biyu da suka gabata, wanda AFRICOM ta bayyana a matsayin wani babban shiri na yaki da ta’addanci a Somaliya.

A cikin watan Fabrairu, hare-haren da Amurka ta kai kan kungiyar IS a Puntland, hukumomin yankin sun  bayar da rahoton cewa an kashe “muhimman mutane”, ko da yake ba su bayar da karin bayani ba.

A wani mataki na kare martabar yankinta da kuma ja da baya kan rarrabuwar kawuna, rahotanni sun ce Somaliya ta bai wa Amurka damar  iko kan muhimman tashoshin jiragen ruwa da sansanonin jiragen sama dake Somaliland da Puntland.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Muna kiran Natasha ta jingine gangamin da za ta yi a Kogi — ’Yan sanda
  • Gwamna Edo Okpebholor Ya Jajantawa Iyalan Wadanda Aka Kashe
  • Gwamna Abba Ya Nemi A Bayyana Fuskokin Waɗanda Suka Kashe ‘Yan Arewa A Edo
  • Muna so a nuna wa duniya mutanen da suka kashe ’yan Arewa a Edo — Gwamnan Kano
  • A Yau Litinin Ce Aka Gudanar Da Sallar Edi Da Bukukuwan Sallah A Nan Iran Da Wasu Kasashen Musulmi
  • Ƴansanda Sun Kama Wanda Ya Kashe Ɗan Bijilanti A Tawagar Sarki Sunusi II
  • Somalia: Harin Amurka a kan kungiyar IS ya kashe wasu mambobin kungiyar
  • Talakawa su girmama shugabanni yayin bayyana matsalolinsu — Sarkin Musulmi
  • Babu tsamin dangantaka tsakaninmu da Gwamnan Sakkwato — Sarkin Musulmi