Iran ta gargadi Amurka kan barazanar harin bam da Trump ya yi
Published: 31st, March 2025 GMT
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta gayyaci mai kula da harkokin kasar Switzerland da ke Tehran domin nuna fishi kan irin munanan ayyukan Isra’ila a yankin da kuma barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ke yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Babban daraktan ma’aikatar harkokin wajen Iran Issa Kameli ne ya gayyaci jami’in diflomasiyyar na Switzerland, wanda kasarsa ke wakiltar muradun Washington a Tehran, yau Litinin.
Kameli ya mika gargadin na Iran a hukumance ga wakilin kasar Switzerland dangane da duk wani aiki na barna tare da bayyana aniyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na mayar da kakkausan martani cikin tsauri kan duk wata barazana.
Jami’in diflomasiyyar na Iran yayi tir da kalaman tunzura tashe-tashen hankula wandanda kuma suka sabawa dokokin kasa da kasa da kuma tsarin Majalisar Dinkin Duniya.
Wakilin na Switzerland ya ba da tabbacin cewa nan take zai isar da sakon Iran ga gwamnatin Amurka.
A ranar Asabar ne Trump ya ce za a kai wa Iran hari idan ba ta kulla yarjejeniya da Amurka ba.
“Idan ba su kulla yarjejeniya ba, za a ji bama-bamai,” in ji shi a wata hira da NBC News. Ya kuma yi barazanar ladabtar da Iran.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
News Fox: Sau 6 Yemen Ta Kakkabo Jiragen Amurka Samfurin Mq 9 A Karkashin Gwamnatin Trump
Tashar talbijin din “News Fox” ta kasar Amurka mai ra’ayin ‘yan mazan jiya ta watsa wani rahoto da yake cewa; Daga lokacin da Donald Trump ya zama shugaban kasa, sau 6 sojojin Yemen su ka kakkabo jiragen sama maras matuki samfurin Mq9.
Rahoton na tashar talabijin din Fox ya kuma yi ishara da yadda sojojin na Yemen su ka kakkabo jirgin sama marasa matuki da marecen juma’a, wanda shi ne karo na 6 tun daga ranar 3 ga watan Maris.
Rahoton ya kuma kara da cewa; Kowane daya daga cikin jiragen sama marasa matuki samfurin mq9 ya kai dalar Amurka miliyan 30.
Bugu da kari rahoton ya kuma bayyana cewa; Sau 35 sojojin Amurka suna kai wa kasar Yemen hare-hare, amma kuma duk da haka har yanzu sojojin Yemen suna ci gaba da kai wa wadannan jiragen na Amurka masu tsada hari. Haka nan kuma sojojin na Yemen suna ci gaba da hana wucewar jiragen ruwa da suke zuwa HKI.
Wannan rahoton kuma ya yi ishara da yadda sojojin na Yemen suke kai wa HKI hare-hare da makamai masu linzami masu cin dogon zango.
Daga fara kai farmakin Aksa zuwa yanzu, adadin jiragen Amurka samfurin MQ 9 da sojojin yemen su ka kakkabo sun kai 16, sai dai wata majiyar ta bayyana cewa, jiragen da sojojin na Yemen su ka kakkabo sun kai 20. Wani jami’in ma’aikatar tsaro ta kasar Amurka ya sanar da tashar talbijin din ta Fox cewa; A 2024 Amurka ta kera, jragen MQ 9 guda 230, amma a kasar Yemen kadai an harbo 16 daga cikinsu.