Jagora : A yau, duniyar musulmi tana bukatar hadin kai
Published: 31st, March 2025 GMT
Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran,Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, ya bayyana cewa yau duniyar musulmi tana bukatar hadin kai fiye da ko wane lokaci.
A yayin ganawarsa da jami’an tsare-tsare da jakadun kasashen musulmi yau Litinin ranar karamar sallah a Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya mayar da hankali kan abubuwan da ke faruwa a yankin inda ya ce a yau wani bangare na duniyar musulmi ya samu munanan rauni.
‘’ Falasdinu ta ji rauni, Lebanon ma ta ji rauni, inji shi. Laifukan da aka aikata a wannan yanki ba a taba ganin irinsa ba, an kashe yara kusan 20,000.”
Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bukaci a hankali tare da daukar nauyin da ya rataya a kan wannan lamari.
“A yau, hakika duniyar musulmi tana bukatar hadin kai inji jagoran.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: duniyar musulmi
এছাড়াও পড়ুন:
Talakawa su girmama shugabanni yayin bayyana matsalolinsu — Sarkin Musulmi
Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su guji cin mutuncin shugabanni yayin da suke bayyana matsalolinsu, inda ya jaddada cewa girmamawa da ladabi suna fi tasiri wajen samun mafita.
“Idan ka zagi shugabanka, ta yaya kake so ya taimaka maka?” in ji shi.
Masar ta miƙa wa Hamas da Isra’ila tayin tsagaita wuta Abubuwan da ya kamata Musulmi ya yi a ranar Karamar Sallah“Amma idan ka yi magana da ladabi, zai saurare ka kuma ya ɗauki mataki.”
Da yake jawabi bayan sallar Idi a Sakkwato, Sarkin Musulmi, ya buƙaci ’yan Najeriya da su ci gaba da yi wa shugabanni addu’a da kuma zaman lafiya da ci gaban ƙasa.
“Ku yi wa Shugaban Ƙasa, Gwamnoni da sauran shugabanni addu’a domin Allah Ya ba su ikon sauke nauyin da ke kansu,” in ji shi.
Ya taya Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan tare da yin kira da su ci gaba da koyi da halaye nagari da suka koya a cikin wata mai alfarma.
Hakazalika, ya jinjina wa malamai kan yadda suka gudanar da wa’azin Ramadan cikin hikima, tare da buƙatar su ci gaba da yaɗa zaman lafiya da haɗin kai a cikin al’umma.