NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Za Su Kwaɗaita Muku Azumtar Sitta Shawwal
Published: 1st, April 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Al-Qur’ani mai girma a cikin suratul Baqarah, Allah Ya wajabta wa musulmi da suka cika wasu sharuɗan azumtar watan Ramadana.
Kamar yadda malamai suka sha faɗi, wannan wata na ɗauke da wasu falala maras misaltuwa da bawa kan samu idan ya maida kai wajen ibada don samun rabauta daga ubangiji.
Kazalika, hadisai sun ruwaito falalar azumtar kwanaki shida na watan Shawwal, watan da ke biye da Ramadan.
NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Komawa Cin Abinci Yadda Ya Kamata Bayan Watan Ramadana DAGA LARABA: Yadda Farashin Kayan Masarufi Suke Gabanin SallahShirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan falalar da ke akwai ga wanda ya azumci kwanaki shidda na watan Shawwal.
Domin sauke shirin, latsa nan.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Sitta Shawwal
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar RED CROSS Ta Duniya Ta Yi Allawadai Da HKI Saboda Kissan Likitoci 8 A Asbitin Rafah
Kungiyar bada agaji ta RED CROSS ta yi allawadai da HKI saboda kissan likitoci 8 a garin Rafah na kudancin gaza a ranar 23 ga watan Maris da muke ciki.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar tana fadar haka a jiya lahadi bayanda aka basu daman dauko gawakin likitocin wadanda suka rasa rayukansu a cikin watan Motar amblance ta daular marasa lafiya.
Labarin ya bayyana cewa lokitocin suna kan hanyarsu ta zuwa unguwar Hashasha inda HKI ta kai hare-hare kan Falasdinawa don basu taimakon gaggawa.
Banda haka sai da aka dauki mako guda cur da kashe likitocin kafin sojojin yahudawan su bada damar a dauki gawakin nasu.
Ya zuwa yanzu dai tun bayan fara yakin Tufanul Aksa falasdinawa dubu 50 da kari ne sojojin HKI suka kashe a gaza.