HKI Ta Sake Kai Wa Unguwar Dhajiya Dake Beirut Hari
Published: 1st, April 2025 GMT
Da safiyar Yau Talata jiragen yakin HKI sun kai hare-hare akan unguwar Dhahiya dake Beirut tare da bayyana cewa ta kai wa wani kusa ne a kungiyar Hizbullah hari.
Harin na yau shi ne irinsa na biyu da HKI ya kai a unguwar Dhahiya tun daga tsagaita wutar yaki a cikin watan Nuwamba na shekarar da ta gabata.
Jiragen yakin na HKI sun yi shawagi a kasa-kasan birnin Beirut kafin aji karar fashewar abubuwa masu karfi.
Kafafen watsa labarai sun ambaci cewa jiragen sun kai harin ne akan wani dogon gini a cikin unguwar.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Lebanon ta sanar da cewa ya zuwa yanzu mutane 3 ne su ka yi shahada,yayin da wasu 4 su ka jikkata.
Masu ayyukan ceto sun nufi wurin da aka hai harin, domin daukar wadanda su ka jikkata zuwa abitocin da suke kusa.
Jotunan farko sun nuna yadda gine-ginen da suke yankin su ka illata, biyu daga cikinsu sun rushe baki daya.
Mazauna yankin sun ce, an kai harin ne a lokacin da mutane suke bacci, lamarin da ya haifar da firgici a tsakaninsu.
A ranar Asabar din da ta gabata dai babban magatakardar kungiyar Hizbulllah Sheikh Na’im Kassim ya yi gargadin cewa, Idan HKI ta ci gaba da keta yarjeniyar tsagaita wuta, sannan kuma ba a taka mata birki ba, to suna da zabin abinda za su yi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojan HKI Ya Halaka A Gaza
Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa sojansu daya ya halaka a Gaza yayin da wasu 4 su ka jikkata bayan da aka kai wa motar da take dauke da su mai sulke hari.
Majiyar ta kuma ce ana ci gaba da yin fada mai tsanani a tsakanin sojojin Isra’ilan da kuma ‘yan gwagwarmaya a yankunan daban-daban na zirin Gaza.
Majiyar Falasdinawa ta ce; ‘yan gwgawarmaya sun tarwatsa wata tankar yakin HKI ta hanyar tashin wani bom da aka ajiye a kan hanya.
An ga jiragen yakin HKI masu saukar angulu suna jigilar daukar wadanda su ka jikkata sanadiyyar harin.
A gefe daya, Falasdinawa da dama sun yi shahada a wasu hare-hare da ‘yan sahayoniya su ka kai akan yankin na Gaza. Tun da safiyar yau Asabar ne dai ‘yan sahayoniyar su ka rika kai hare-haren wanda ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 30.