Arakci: Abokan Gaba Za Su Yi Nadamar Yi Wa Iran Barazana
Published: 1st, April 2025 GMT
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Arakci ya bayyana cewa, duk wata barazana da za a yi wa Iran za ta sa makiya su yi babbar nadama.
A wata hira a tashar talabijin din almasirah ta kasar Yemen ta yi da shi, ministan harkokin wajen na Iran ya ce, farfagandar da ake yi ta cewa, kai wa kasar Yemen hari share fage ne na yaki da Iran ba sabon abu ba ne, an sha yin irin wannan barazanar a baya.
Abbas Arakci ya kara da cewa; Iran ba za ta taba kyale duk wani mahaluki da zai rika yin Magana da ita da harshe na barazana ba, sannan ya kara da cewa makiya za su yi nadamar wannan barazanar.
Da yake Magana akan cigaba da kai wa Yemen hare-hare da Amurkan take yi, ministan harkokin wajen na Iran ya ce, nasarar da Yemen din take samu ne ya sa hakan take faruwa,kuma a cikin shekaru 10 na hare-haren da ake kai wa Yemen har yanzu an kasa yin galaba akan ta.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ruftawar gini ta kashe mutum 5 a Legas
Kawo yanzu an samu aƙalla mutum biyar da suka riga mu gidan gaskiya a sanadiyyar ruftawar wani bene mai bene mai hawa uku da ya ruguje a unguwar Ojodu-Berger da ke Jihar Legas.
Haɗarin ya faru ne da misalin ƙarfe 09.45 na safiyar ranar, inda hukumar kai ɗauki gaggawa tare da taimakon ’yan sanda suka gano cewa wani gini mai hawa uku ɗauke da gidan abinci da mashaya ne ya ruguje.
Mayaƙan ISWAP sun tarwatsa gada a Yobe Kada Kanawa su bari rigingimun siyasa su hana su zaman lafiya — ShettimaJami’in hukumar bayar da agajin, Ibrahim Farinloye, ya ce daga faruwar lamarin zuwa yanzu an ceto mutane 20 jimilla da suka maƙale a ƙarƙashin baraguzai.
“Sai dai abin takaicin shi ne cikin gawawwakin mamatan biyar da aka samu akwai mata uku da maza biyu.”
Shi ma da yake nasa jawabin a ranar Lahadi, babban Sakataren hukumar LASEMA, Olufemo Oke-Osanyintolu, ya ce mamatan biyar da aka samu an killace su a ɗakin ajiyar gawawwaki na asibiti.
Da farko dai babu labarin mutuwa, sai dai an samu asarar dukiya, amma yanzu bayan ci gaba da aikin ceto, an gano gawawwaki a cikin waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin baraguzai.
’Yan sanda da hukumar kai dauƙin gaggawa sun ci gaba da bincike domin gano musabbabin rugujewar ginin.
Jami’ai na hukumar LASEMA na ci gaba da binciken baraguzan ginin da nufin gano ko da sauran mutane a ciki.