Mai bai wa jagoran juyin musulunci na Iran shawara Dr. Ali Larijani ya ce, idan har Amurka da Isra’ila su ka fake da batun shirin makamashin Nukiliyar Iran na zaman lafiya, su ka kawo mata hari, to ya zama wajibi a gare ta ta kera makaman Nukiliya.

Dr. Ali Larijani wanda tashar talabijin din Iran ta yi jira da shi a jiya Litinin da dare, ya bayyana cewa; manyan kasashen duniya suna son yin alaka kai tsare da Iran cikin ‘yanci, sai dai suna da fuskantar matsin lamba daga Amurka.

Tsohon shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran ya kuma kara da cewa; Idan har Amruka da HKI su ka kawo wa Iran hari, to, za ta dau hanyar kera makaman Nukiliya, kuma su kansu al’ummar kasa abinda za su so ganin ya faru kenan.

Dr. Ali Larijani wanda memba ne a cikin majalisar fayyace maslahar tsaron musulunci, ya kara da cewa; Yaki da Iran ba abu ne mai sauki ba, yana da tattare da hatsarin da zai koma kan mahara.

Larijani ya kuma ce; Fatawar Jagora ita ce, ta haramta mallakar makamin Nukiliya,amma idan Amurka ta yi kuskure, to matsin lambar mutane zai sa Iran ta kama hanyar kera makaman Nukiliya.

Har ila yau, Larijani ya ce; Fasahar Nukiliya da Iran take da ita, an tsara ta akan cewa, ko da an kawo wa Iran din hare-hare, to za ta ci gaba da aiki ba tare da tsaiko ba. Kum su kansu masu hankali daga cikin makiya sun san cewa idan su ka kawo wa Iran farmaki, to kuwa za ta daura damarar kera makaman Nukiliya.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kera makaman Nukiliya

এছাড়াও পড়ুন:

Gharibabadi : inganta sinadarin uranium jan layi ne a tattaunawar Iran da Amurka

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa tace uranium din ta tamakar jan layi ne a tattaunawar dake wakana tsakaninta da Amurka.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar ne Kazem Gharibabadi ya bayyana hakan, inda ya ce hakkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne inganta sinadarin Uranium, yana mai jaddada cewa, wannan batu a matsayin jan layi a tattaunawar da Amurka.

Mista Gharibabadi ya bayyana haka ne a yayin taron kwamitin majalisar dokoki kan tsaron kasar da manufofin ketare, inda ya yi wa ‘yan majalisar bayani kan shawarwari zagaye na biyu tsakanin Tehran da Washington, wanda ya gudana a Rome, babban birnin kasar Italiya.

Jami’in na iran ya kara da cewa tawagar kasar ta jaddada matsayinta na cewa Iran ba ta neman kera makaman kare dangi, inda ya bayyana cewa ayyukan nukiliyar Iran na zaman lafiya ne gaba daya.

Mataimakin ministan harkokin wajen na Iran ya kuma jaddada cewa, daya daga cikin manyan makasudin shawarwarin shi ne cimma nasarar dage takunkumin da aka sanya wa iran gaba daya da suka hada da na majalisar dokokin Amurka da kuma umarnin zartarwar takunkuman matsin lamba da shugaba Donald Trump ya sanya wa hannu.

Kawo yanzu AMurka da Iran sun gudanar da shawarwari har guda biyu ka batun shirin nukiliyar kasar ta Iran, kuma dukkan bagarorin sun bayyana tattaunawar da mai kyakyawan fata.

A ranar Asabar mai zuwa bagarorin zasu sake ganawa a karo na uku, bayan wacce sukayi a Oman da kuma Italiya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Ba Ta Da Niyyar Tattaunawa Da Amurka A Fili Bainar Jama’a Kan Shirinta Na Makamashin Nukiliya
  • Iran Ta Jaddada Matsayinta Kan Batun Tace Sinadarin Yuranium A Batun Tattaunawa Da Amurka
  • Gharibabadi : inganta sinadarin uranium jan layi ne a tattaunawar Iran da Amurka
  • Gaza : Red Crescent ta yi watsi da rahoton Isra’ila kan kisan da aka yi wa jami’an agaji
  • Idan Shugaban Kasar Siriya Mai Ci Ya Taka Kasar Iraki Ana Iya Kama Shi
  • Tawagar Gwamnati Ta Kai Ziyara Filato, Ta Sha Alwashin Kawo Karshen Kashe-kashe A Jihar
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yaba Da Zaman Tattaunawan Iran Da Amurka Zagaye Na Biyu A Birnin Roma
  • Ma’aikatar Lafiya Ta Yemen Ta Sanar Da Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada A Hare-Haren Amurka Kan Kasar
  • Ma’aikatar Kasuwancin Sin: Dole Ne Amurka Ta Daina Dora Laifi Kan Sauran Kasashe
  •  Abbas Arakci: Tattaunawa Da Amurka Ta Hanyar Shiga Tsakanin Oman Ta Shiga Sabon Zango