SALLAH KARAMAH: Ku Sadaukar Don Daukakar Addini, HRH Idi Chiroma
Published: 1st, April 2025 GMT
Mai Martaba Idi Chiroma, Sarkin Gassol a Jihar Taraba, ya ce Musulmin da suka gudanar da azumin watan Ramadan na shekarar 2025 sun nuna tsayin daka wajen sadaukarwa ga addini.
Chiroma ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake jawabi ga al’ummar Musulmi a wani bangare na bikin Sallar karama a karamar hukumar Gassol da ke jihar.
Ya kuma ja hankalin al’ummarsa da su jure duk wani kalubalen da suka fuskanta yayin da suka jure mawuyacin hali na baya-bayan nan domin ibada.
Chiroma ya bayyana cewa wadanda za su koma ga tsohon halin da suke ciki na iya zama ba tare da albarkar da ke tattare da azumin watan Ramadan ba.
Ya kuma yi kira ga al’ummarsa da su ci gaba da tsoron Allah don samun ladan da ke ciki.
Mai martaba Sarkin wanda shi ne mai daraja ta biyu a Jihar Taraba, ya gode wa Gwamna Agbu Kefas kan yakin da ya yi na tabbatar da tsaro da tsaron mutanen Gassol.
Bugu da kari, Chiroma ya yabawa al’ummar yankinsa bisa hadin gwiwa da jami’an tsaro domin kawo karshen sace-sacen mutane da ‘yan fashi a yankin.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Gassol da su ci gaba da zama lafiya da juna.
An bayyana cewa an gudanar da sallar karama lami lafiya a dukkanin kananan hukumomin jihar Taraba goma sha shida da suka hada da Gassol.
Sani Sulaiman
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Taraba
এছাড়াও পড়ুন:
Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Bada Tallafin Kudi Ga Manoman Alkama
Shugaban karamar hukumar Birnin Kudu, Alhaji Muhammad Uba Builder, ya sake jaddada kudirinsa na kyakkyawan shugabanci wajen gudanar da harkokin karamar hukumar.
Ya bada wannan tabbaci ne yayin rabon Naira dubu hamsin hamsin ga mutane 70 da suka amfana da shirin noman alkama da karamar hukumar ta kirkiro.
A cewarsa, mutane 165 ne aka saka cikin shirin, inda matasa 70 daga ciki ‘yan siyasa ne, wadanda a ke da bukatar canza rayuwarsu zuwa hanyoyin neman na kai, duba da cewa siyasa ba sana’a ba ce, illa tsarin shugabanci ne.
Alhaji Muhammad Uba Builder ya ce an samar wa mahalarta shirin da filin noma, tare da gyaran filin, da samar da irin alkama da sauran abubuwan bukata, yayin da suke lura da gonakin har zuwa lokacin girbi.
Ya ce kasancewar wadannan ‘yan siyasa sabbin shiga harkar noma ne yasa ba su samu gagarumar nasara ba, don haka akwai bukatar a kara tallafa musu da jari domin su shiga kananan sana’o’i, yayin da karamar hukumar za ta hada kai da hukumar manoma da makiyaya domin samar musu da kadada daya ta noma ga kowanensu domin su yi noma na damina.
Shugaban ya bukaci jama’a da su yi watsi da jita-jita, su kasance masu juriya, da addu’a ga shugabanni domin su gudanar da aikinsu bisa adalci da gaskiya.
Da suke magana a madadin ‘yan siyasa, Usman Sarki da Bello Ajayi sun sake jaddada kudurinsu na kare mutuncin jihar da shugaban karamar hukumar tare da alkawarin shiga harkokin da za su inganta rayuwarsu ta tattalin arziki.
Usman Muhammad Zaria