Tsohon Gwamnan Zamfara Ya Bukaci A Ci Gaba Da Tallafawa Mabukata Bayan Ramadan.
Published: 1st, April 2025 GMT
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma, Dakta Abdul’aziz Yari, ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu na alheri fiye da watan Ramadan.
Da yake zantawa da manema labarai a mahaifarsa Talatan Mafara, a wani bangare na sakonsa na Sallah, Yari ya jaddada muhimmancin ci gaba da al’adun bayar da Zakka, Sadaka, da sauran nau’o’in tallafi ga marasa galihu a duk shekara.
Ya yabawa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa bullo da shirye-shiryen jin dadin jama’a da nufin inganta rayuwar ‘yan Najeriya.
Dokta Yari ya yi kira ga ‘yan kasar da su ba da cikakken goyon baya ga kokarin shugaban kasar na ciyar da kasar gaba.
“A madadin ‘ya’yan jam’iyyar APC na Zamfara da al’ummar mazaba ta, na mika sakon taya murna ga shugaba Tinubu na cika shekaru 73 da haihuwa. “Muna addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya kara masa shekaru masu yawa cikin koshin lafiya, da wadata, da kuma hikimar da zai jagoranci kasar nan ta hanyar da ta dace. Za mu ci gaba da yi masa addu’ar samun nasara a matsayinsa na shugaban kasa,” inji shi.
COV/AMINU DALHATU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Zamfara
এছাড়াও পড়ুন:
Arakci: Abokan Gaba Za Su Yi Nadamar Yi Wa Iran Barazana
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Arakci ya bayyana cewa, duk wata barazana da za a yi wa Iran za ta sa makiya su yi babbar nadama.
A wata hira a tashar talabijin din almasirah ta kasar Yemen ta yi da shi, ministan harkokin wajen na Iran ya ce, farfagandar da ake yi ta cewa, kai wa kasar Yemen hari share fage ne na yaki da Iran ba sabon abu ba ne, an sha yin irin wannan barazanar a baya.
Abbas Arakci ya kara da cewa; Iran ba za ta taba kyale duk wani mahaluki da zai rika yin Magana da ita da harshe na barazana ba, sannan ya kara da cewa makiya za su yi nadamar wannan barazanar.
Da yake Magana akan cigaba da kai wa Yemen hare-hare da Amurkan take yi, ministan harkokin wajen na Iran ya ce, nasarar da Yemen din take samu ne ya sa hakan take faruwa,kuma a cikin shekaru 10 na hare-haren da ake kai wa Yemen har yanzu an kasa yin galaba akan ta.