Haka kuma, an Ƙwato bindiga ƙirar gida da Naira miliyan 4.84 da ake zargin kuɗin fansa ne.

An ceto Dokta Yushau ba tare da wata matsala ba.

A wata arangama daban, jami’an ‘yansanda sun kama wani Kafinta Musa a Jihar Taraba bisa zargin fashi da makami, garkuwa da mutane, da mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba.

An ƙwato bindiga ƙirar AK-49 a hannunsa, kuma ana ci gaba da bincike don kama sauran miyagun da ke tare da shi.

Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya jinjina wa jami’an da suka gudanar da wannan aikin tare da kira ga al’umma da su ci gaba da ba da bayanan sirri da za su taimaka wajen yaƙi da laifuka.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Yansanda Garkuwa Taraba

এছাড়াও পড়ুন:

Mutane 9 Sun Mutu Sanadin Haɗarin Mota A Katsina

A wani hatsarin mota da ya faru a hanyar Malumfashi-Kafur a Jihar Katsina, mutane tara sun rasu yayin da wasu 11 suka jikkata. Hatsarin dai ya shafi wata babbar motar bas da ke ɗauke da fasinjoji 20. 

Aliyu Ma’aji, Kwamandan Hukumar Kiyaye  Haɗɗura ta ƙasa (FRSC) a jihar, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi. Ya bayyana cewa binciken da hukumar ta gudanar ya nuna cewa gaggawar tuki ne ya haifar da hatsarin, inda direban ya rasa ikon sarrafa motar.

An Gabatar Da Motar Asibiti Ta Farko Mai ISO Na Matsayin Kasa Da Kasa A Hukumance Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin Mutane 2 A Kano – FRSC

Haɗarin ya yi sanadin mutuwar mutane tara da ke cikin wata babbar motar bas mai ɗauke da fasinjoji 20, yayin da aka ceci wasu 11 kuma ana jinyar su a asibiti,” in ji Ma’aji. Ya kuma yi kira ga direbobi su guje wa tuƙin gaggawa, jigilar fasinjoji fiye da kima da kuma rashin kulawa yayin lokutan bukukuwa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mutum 2 sun rasu, 13 sun ɓace a hatsarin jirgin ruwa a Bayelsa
  • Basakkwacen da ya yi ridda ya sake karɓar addinin Musulunci
  • ‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga, Sun Ceto Ɗalibai 2 A Nasarawa
  • Kasar Sin Za Ta Yi Ramuwar Gayya Kan Takunkumin Biza Da Amurka Ta Kakaba Wa Jami’anta
  • Ma’aikatan Kasar Sin Sun Ceto Mutum 8 Zuwa Yanzu A Myanmar
  • Duk Da Hanin Gwamna Da ‘Yansanda, Natasha Ta Isa Gida Kuma Ta Yi Taro
  • Ta zuba wa abokan aikinta guba bayan taƙaddama kan ƙarin matsayi
  • Iran Ta Ce Tattaunawa Da Amurka Tare Da Mai Shiga Tsakani Na Gaba, Ya Danganci Matakan Da Ta Dauka Kan Iran
  • Mutane 9 Sun Mutu Sanadin Haɗarin Mota A Katsina