Aminiya:
2025-04-02@17:41:03 GMT

Muna kiran Natasha ta jingine gangamin da za ta yi a Kogi — ’Yan sanda

Published: 1st, April 2025 GMT

Rundunar ’yan sanda ta nemi da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta jingine shirinta na kai ziyara da zummar hada gangamin bikin Sallah a Jihar Kogi.

Wata sanarwa da kakakin ’yan sandan Jihar Kogi, ASP William Aya ya fitar, ta ambato Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP William Ɗantawaye na cewa gangamin ya ci karo da haramcin gudanar da gangamin siyasa da gwamnatin jihar ta yi ranar Litinin.

HOTUNA: Abba da Gwamnan Edo sun ziyarci iyalan mafarautan da aka kashe a Edo Ta zuba wa abokan aikinta guba bayan taƙaddama kan ƙarin matsayi

“A sakamakon rahoton sirri kan barazanar tsaro a jihar Kogi da ya sanya hana duk wani gangami da jerin gwano da gwamnatin jihar Kogi ta yi, rundunar ‘yan sandan na kira ga wadanda suka shirya gangamin a Okene da su jingine irin wannan taron domin samar da zaman lafiya a Jihar Kogi.

Sanarwar ta ce, “kiran a jingine gangamin ya zama dole ne bisa rahotannin sirri da muka samu dangane da ƙoƙarin wasu ɓata gari na karkatar da gangamin zuwa wani abu daban da ka iya jefa jihar cikin tashin hankali.

“Saboda haka rundunar ’yan sandan ba za ta zura ido ta bar duk wani abun da zai jefa jihar mai zaman lafiya zuwa tashin hankali ba,” in ji sanarwar.

A watan da ya gabata ne dai zauren Majalisar Dattawan Nijeriya ya dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan bisa zargin rashin da’a, kan sauya mata matsugunni da ta ce an yi ne ba bisa ka’ida ba kuma tta alakanta shi da zargin da take yi wa shugaban majalisar, Godswill Akpabio da cin zarafi da neman ta da lalata.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnan Edo Ya Ziyarci Sanata Barau Kan Kisan Yan Arewa 16

Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya kai ziyara ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, domin nuna alhini kan kisan gilla da aka yi wa matafiya dyan Arewa a Uromi. Harin da aka kai a ranar Alhamis ya haifar da mutuwar mafarauta da ke kan hanyar zuwa bikin Sallah. Gwamnan ya bayyana cewa an kama mutane 14 da ake zargi da hannu a kisan, kuma za a kai su Abuja domin ci gaba da bincike.

A yayin ziyarar, Gwamnan Okpebholo ya yi alkawarin cewa gwamnatin jihar za ta taimaka wa iyalan wadanda aka kashe, yana mai nuni da cewa Shugaban kasa da Yansanda sun dauki matakai kan lamarin. “Za mu tabbatar an gurfanar da wadanda suka aikata wannan mugun aiki a gaban doka,” in ji Gwamnan. Sanata Barau ya amsa da yabon matakan gwamnatin Edo, yana mai cewa: “Dole ne a ci gaba da yin Adalci domin hana irin wannan bala’i a nan gaba.”

Yadda ‘Yan Banga A Edo Suka Yi Sanadin Kashe Matafiya Mafarauta 16 – Direban Motar YANZU-YANZU: Gwamnan Edo Ya Kai Ziyarar Jaje Kan Kisan Mafarauta A Uromi

‘Yansandan sun kara da cewa za su ci gaba da yaki da duk wani yunkurin tayar da tarzoma a jihar. Gwamnan Edo ya kuma yi kira ga al’umma da su yi haƙuri, yana mai jaddada cewa jihar ba ta yarda da ‘yan daba ko dakar doka a hannu ba. “Edo ta kasance gida ne na zaman lafiya ga dukkan al’ummar Nijeriya, kuma za mu kiyaye wannan tarihi,” in ji Gwamnan

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Duk Da Hanin Gwamna Da ‘Yansanda, Natasha Ta Isa Gida Kuma Ta Yi Taro
  • Babu dokar da na karya saboda yin taro a mazaɓata — Natasha
  • Babu dokar da na karya saboda yin taron a mazaɓata — Natasha
  • Sarki Sanusi Ya Yabawa Gwamna Yusuf Kan Manufofin Habaka Jama’ar Kano
  • Gangamin da zan yi a mazaɓata babu fashi — Natasha
  • NUJ Kebbi Tayi Kiran Ayi Bukukuwan Sallah Lafiya
  • Muna jiran ganin hukuncin da za a ɗauka kan kashe ’yan Arewa a Edo — Sarkin Musulmi
  • Gwamnan Edo Ya Ziyarci Sanata Barau Kan Kisan Yan Arewa 16
  • Matashi ya kashe jami’in tsaron Sarki Sanusi II a Kano