HOTUNA: Sarki Sanusi ya kai wa Gwamna Abba ziyarar barka da Sallah
Published: 1st, April 2025 GMT
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi baƙuncin Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, a fadar gwamnatin jihar.
Sarkin dai ya kai wa gwamnan ziyarar ce kamar yadda aka saba a Hawan Nassarawa da ake gudanarwa bisa al’ada duk shekara.
Sai dai a sakamakon haramcin gudanar da haye-hayen sallah da rundunar ’yan sandan jihar ta yi, Sarkin bai cika duk tsare-tsaren da al’ada ta tanada ba na gudanar da Hawan Sallah.
Aminiya ta ruwaito cewa, Sarkin wanda ya yi ƙoƙarin kawar da idon jama’a, ya bi ta wasu hanyoyin da ba su aka saba bi wajen kai wa gwamna ziyara a yayin gudanar da hawan cikakke.
Haka kuma, Sarkin ya yi amfani da jerin gwanon motoci ƙalilan maimaiko hawa dawakai
Sai dai an tsananta tsaro a duk hanyoyin da Sarkin ya bi tun daga Fadar Sarki ta Gidan Ƙofar har zuwa Gidan Gwamnatin Kano.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Hawan Nasarawa Jihar Kano Sarki Sanusi II
এছাড়াও পড়ুন:
Dalilin da muka soke Hawan Bariki — Masarautar Zazzau
Masarautar Zazzau ta sanar da soke Hawa Bariki a wannan sallar ta bana — daya daga cikin haye-hayen shagulgulan Sallah na al’ada da masarautar ke gudanarwa a washegarin idin karamar Sallah.
A bisa al’adar Hawan Bariki, Sarkin Zazzau ya kan kai wa Gwamna gaisuwar sallah tare da duk hakimansa yayin da mazauna za su yi dakon wadanda ke haye-hayen dawakan a gefen titi su ma suna yi wa Sarki gaisuwar ban girma.
Nijar ta fice daga rundunar MNJTF mai yaƙi da masu iƙirarin jihadi NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Komawa Cin Abinci Yadda Ya Kamata Bayan Watan RamadanaSarki yakan jagoranci tawagar masarautar ta Zazzau inda zai ratsa ta cikin garin Zazzau sannan ya shiga unguwar Sabon Gari inda zai ziyarci Gwamna a gidan da aka tanada tun zamanin turawan mulkin mallaka.
Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawun Masarautar Zazzau, Abdullahi Aliyu Kwarbai ya fitar, ya ce an soke hawan sakamakon dalilai na aikin gyaran titi da shimfida sabuwar kwalta da ake yi a kan hanyar Kofar Doka zuwa kwanar Agoro.
Ya ce wannan aikin hanya da ake kan yi zai kawo cikas ga masu haye-hayen dawakai da kuma al’umma baki daya.
“Saboda haka wannan shi ne dalilin da Masarautar Zazzau ta soke Hawan Barikin da ake gudanar a washegarin Sallah karama” a cewar sanarwar.