Haaland zai yi jinyar mako bakwai — Guardiola
Published: 1st, April 2025 GMT
Kociyan Manchester City, Pep Guardiola, ya ce ɗan wasan gaban ƙungiyar, Erling Haaland, zai yi jinyar mako bakwai a sakamakon raunin da ya samu a idon sahunsa a wasan kofin FA da ƙungiyar ta fafata da Bournemouth a ranar Lahadi.
Ɗan wasan na ƙasar Norway bai ƙarasa wasan ba, inda aka cire shi a minti 61 da fara wasan bayan ya farke ƙwallo ɗaya, kafin daga bisani City ta doke Bournemouth da ci biyu da ɗaya domin zuwa wasan kusa da na ƙarshe.
Tun a jiya Litinin ce City ta ce Haaland zai ga ƙwararren likita saboda raunin da ya ji rauni, kuma tana sa ran zai warware ya ci gaba da taka leda a wannan kakar da ake ciki.
Sai dai a yau Talata gabanin wasan da City za ta fafata da Leicester City a Firimiyar Ingila, Guardiola ya sanar da cewa likitocin sun tabbatar da cewa ɗan wasan zai yi jinyar mako biyar zuwa bakwai kafin ya iya dawowa taka leda a Etihad.
A bayan nan dai City na fuskantar cakwakwiyar ’yan wasa da ke fama da jinya, ciki har da Rodri wanda ya lashe kambun gwarzon ɗan wasa ta Balon d’Or a bara.
A yanzu dai City ba ta wani ɗan wasa da zai iya maye gurbin Haaland, amma Guardiola ya ce ƙungiyar za ta ƙarasa kakar wasannin a daddafe a haka kuma za ta jajirce don samun gurbin zuwa Gasar Zakarun Turai mai zuwa.
A halin yanzu City mai maki 48 na mataki na biyar a teburin Firimiyar Ingila yayin da ya rage mata wasanni tara da kuma wasan mataki na biyun ƙarshe a Kofin FA da za ta kece raini da Nottingham Forest a wannan wata na Afrilu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Erling Haaland Pep Guardiola
এছাড়াও পড়ুন:
Duk Da Hanin Gwamna Da ‘Yansanda, Natasha Ta Isa Gida Kuma Ta Yi Taro
Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, da aka dakatar, ta bayyana cewa “ita ba mahaukaciya ba ce”, kuma “ba ta tsoron kowa” a yayin da take jawabi ga dimbin magoya bayanta a lokacin da ta dawo gida a Ihima, karamar hukumar Okehi ta jihar Kogi a ranar Talata da yamma. Dawowarta ta zo ne a daidai lokacin da ake cike da rikicin siyasa, domin tun da farko gwamnatin jihar Kogi da rundunar ‘yansandan jihar ta kafa dokar hana tarukan jama’a, saboda dalilan tsaro. Sannan kuma, shugaban karamar hukumar Okehi, Hon. Amoka Eneji, ya kuma sanya dokar hana fita a karamar hukumar a wani yunkuri na dakatar da shirin dawowar Natasha gida a yayin bukukuwan Sallah tare da al’ummar mazabarta. Gwamnatin Edo Za Ta Biya Diyyar Mafarauta ‘Yan Kano 16 Da Aka Kashe A Uromi BUK Ta Ƙaddamar Da Shafin Intanet Da Ɗalibai Za Su Ke Duba Sakamakon Jarrabawa Amma, ta bijirewa umarnin gwamnati, Natasha ta isa gidanta na Ihima a cikin wani jirgi mai saukar Angulu da misalin karfe 1:00 na ranar Talata, inda dimbin magoya bayanta suka taru a gidanta tun da safiyar karfe 7:00 suna jiran isowarta. Da take yi wa magoya bayanta jawabi, Natasha ta fara da bayyana farin cikinta na dawowa gida. “Ina bukatarku duka ku kula da abin da zan fada, gida akwai dadi. “Na ji daɗi da na dawo gida. Kuma babu wanda zai iya hana ni zuwa gida. “Ni Ebira ce, Dr. Akpoti mahaifina ne, na san gidana, ni ba mahaukaciya ba ce,” in ji ta.Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp