Sarki Sanusi Ya Yabawa Gwamna Yusuf Kan Manufofin Habaka Jama’ar Kano
Published: 1st, April 2025 GMT
Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, a ranar Talata ya yaba wa Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano bisa bayar da fifiko akan ilimi, kiwon lafiya, noma, da tsaro a jihar. Sarki Sanusi II ya bayyana jin dadinsa ne a lokacin da ya kai gaisuwar Sallah ga gwamnan Kano, kamar yadda aka saba gudanarwa a al’adance duk shekara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman Kano
An yi jana’izar marigayi Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sunusi, a Fadar Sarkin Kano da ke Kofar Kudu, inda dubban jama’a suka halarta.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, sun halarci jana’izar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sunusi.
Basakkwacen da ya yi ridda ya sake karɓar addinin Musulunci Tinubu zai tafi ziyarar makonni biyu a FaransaAn gudanar da sallar jana’izar ne a Fadar Sarkin Kano da ke Kofar Kudu, inda Farfesa Sani Zahradden ya jagoranci sallar.
Dubban jama’a ne suka halarci jansiza5 marigayin.
Har ila yau, Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi II, ya halarci jana’izar.
Marigayi Alhaji Abbas Sunusi, ya rasu ne a daren ranar Talata a gidansa da ke Kano bayan doguwar jinya.
Ya rasu yana da shekara 92 a duniya.
An birne shi a makabartar Gandun Albasa.
Domin nuna alhini game da rasuwar marigayin, Gwamnatin Jihar Kano da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, sun dakatar da bukukuwan Sallar da suka shirya gudanarwa a yau Laraba.
Marigayi Galadima ya riƙe mukami mafi girma a Masarautar Kano, kuma shi ne mahaifin Abdullahi Abbas, Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano.
Ga hotunan yadda jana’izar ta gudana: