Wang Yi Ya Jinjina Wa Gudummawar Da Sinawa Da ’Yan Rasha Suka Bayar A Yakin Duniya Na Biyu
Published: 2nd, April 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, ya bayyana a yau Talata cewa, al’ummar Sinawa da ’yan kasar Rasha sun ba da gudummawa gaya wajen samun nasarar yakin duniya na biyu.
A wata hira da ya yi da rukunin gidajen rediyo da talabijin mallakin kasar Rasha wato Russia Today a yau a birnin Moscow, Wang ya bayyana cewa, bana shekara ce ta cika shekara 80 da samun nasarar yakin da Sinawa suka gwabza na tirjiya a kan zaluncin kasar Japan, da kazamin yakin kishin kasa na Tarayyar Soviet, da kuma yakin duniya na biyu.
Wang, ya yi kira ga kasashen biyu da su tsaya tsayin daka wajen tabbatar da adalci a matakin kasa da kasa yayin da ake fuskantar manyan sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba cikin karni guda a duniya, tare da hada karfi da dukkanin al’ummomin duniya masu son zaman lafiya, wajen kare tarihin da aka kafa ta hanyar zubar da jini da asarar rayuka, da kuma adawa da duk wani yunkuri ko mataki na musantawa, ko murgudawa, ko sake fasalin tarihin yakin duniya na biyu.
Ya bukaci kasashen biyu da su kiyaye tsarin kasa da kasa da aka kafa bayan yakin, da daukar bikin cika shekara 80 da kafa Majalisar Dinkin Duniya a matsayin wata dama ta tabbatar da iko da matsayin majalisar ta duniya, da aiwatar da hakikanin tsarin da ya kunshi bangarori daban-daban, da karfafa bin manufofi da ka’idojin yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya sau da kafa ga dukkan kasashe. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: yakin duniya na biyu
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Ta Nanata Adawa Da Matakan Tilastawa Da Nuna Babakeren Tattalin Arziki
Ya ce, bisa tagomashin katafariyar kasuwarta, da kyawawan manufofin da ake tsammani, da ingantaccen yanayin kasuwanci, Sin na ci gaba da zama kasa mai albarka ga kamfanonin kasa da kasa su zo su zuba jari domin samun bunkasa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp