Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, da aka dakatar, ta bayyana cewa “ita ba mahaukaciya ba ce”, kuma “ba ta tsoron kowa” a yayin da take jawabi ga dimbin magoya bayanta a lokacin da ta dawo gida a Ihima, karamar hukumar Okehi ta jihar Kogi a ranar Talata da yamma. Dawowarta ta zo ne a daidai lokacin da ake cike da rikicin siyasa, domin tun da farko gwamnatin jihar Kogi da rundunar ‘yansandan jihar ta kafa dokar hana tarukan jama’a, saboda dalilan tsaro.

Sannan kuma, shugaban karamar hukumar Okehi, Hon. Amoka Eneji, ya kuma sanya dokar hana fita a karamar hukumar a wani yunkuri na dakatar da shirin dawowar Natasha gida a yayin bukukuwan Sallah tare da al’ummar mazabarta. Gwamnatin Edo Za Ta Biya Diyyar Mafarauta ‘Yan Kano 16 Da Aka Kashe A Uromi  BUK Ta Ƙaddamar Da Shafin Intanet Da Ɗalibai Za Su Ke Duba Sakamakon Jarrabawa Amma, ta bijirewa umarnin gwamnati, Natasha ta isa gidanta na Ihima a cikin wani jirgi mai saukar Angulu da misalin karfe 1:00 na ranar Talata, inda dimbin magoya bayanta suka taru a gidanta tun da safiyar karfe 7:00 suna jiran isowarta. Da take yi wa magoya bayanta jawabi, Natasha ta fara da bayyana farin cikinta na dawowa gida. “Ina bukatarku duka ku kula da abin da zan fada, gida akwai dadi. “Na ji daɗi da na dawo gida. Kuma babu wanda zai iya hana ni zuwa gida. “Ni Ebira ce, Dr. Akpoti mahaifina ne, na san gidana, ni ba mahaukaciya ba ce,” in ji ta.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sarki Sanusi Ya Yabawa Gwamna Yusuf Kan Manufofin Habaka Jama’ar Kano

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, a ranar Talata ya yaba wa Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano bisa bayar da fifiko akan ilimi, kiwon lafiya, noma, da tsaro a jihar. Sarki Sanusi II ya bayyana jin dadinsa ne a lokacin da ya kai gaisuwar Sallah ga gwamnan Kano, kamar yadda aka saba gudanarwa a al’adance duk shekara. Sin Da Zambiya Sun Daddale Yarjejeniyar Fitar Da Kwarurun Macadamia Nuts Farashin Man Fetur Ya Ƙara Tashi Sakamakon Rikicin Dangote Da NNPCL “Mun zo ne domin mika gaisuwar mu ta barka da Sallah tare da gode muku bisa gagarumin aikin da kuke yi, musamman a fannin ilimi da noma, inda kuka samar da tallafin kayan aikin noma na zamani. “Muna godiya ga Allah da ya ba mu damar shaida wannan lokaci na musamman, inda muke taruwa don sake gaishe da Gwamna a yayin bikin Sallah,” in ji shi. Sanusi ya yabawa ‘yan majalisar dokokin jihar Kano bisa bin doka da oda da suka yi, wanda ya ce ya dawo da tsari da kimar masarautar. “Muna fatan gwamnan zai ci gaba da yin aiki mai kyau, kuma muna kira ga shugabannin kananan hukumomin da su yi koyi da shi, su kara kaimi,” in ji Sarkin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Babu dokar da na karya saboda yin taro a mazaɓata — Natasha
  • Babu dokar da na karya saboda yin taron a mazaɓata — Natasha
  • Sarki Sanusi Ya Yabawa Gwamna Yusuf Kan Manufofin Habaka Jama’ar Kano
  • HOTUNA: Sarki Sanusi ya kai wa Gwamna Abba ziyarar barka da Sallah
  • Gangamin da zan yi a mazaɓata babu fashi — Natasha
  • Muna kiran Natasha ta jingine gangamin da za ta yi a Kogi — ’Yan sanda
  • ‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa
  • Gwamna Edo Okpebholor Ya Jajantawa Iyalan Wadanda Aka Kashe
  • Gwamna Abba Ya Nemi A Bayyana Fuskokin Waɗanda Suka Kashe ‘Yan Arewa A Edo