Ma’aikatan Kasar Sin Sun Ceto Mutum 8 Zuwa Yanzu A Myanmar
Published: 2nd, April 2025 GMT
Tawagogin ma’aikatan ceto na kasar Sin na ci gaba da aiki a yankin da ya fi shan wuya na Mandalay da ke tsakiyar kasar Myanmar, sakamakon girgizar kasar da ta afku mai karfin maki 7.9 a makon da ya gabata, inda zuwa yanzu suka ceci mutum takwas da suka tsira daga ibtila’in, da misalin karfe 8 na safiyar ranar Talata, agogon kasar.
A yayin bikin bayar da gudummawar kudi ga wadanda girgizar kasar ta shafa a birnin Nay Pyi Taw a yau Talata, shugaban majalisar gudanarwar kasar Myanmar, Min Aung Hlaing, ya ce, mutanen da suka mutu sakamakon mummunar girgizar kasar wacce ta afku a kasar a ranar Jumma’a, sun kai 2,719, yayin da wasu 4,521 suka jikkata, kana 441 suka bace ba a ji duriyarsu ba har yanzu, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sin Da Zambiya Sun Daddale Yarjejeniyar Fitar Da Kwarurun Macadamia Nuts
A jiya Litinin ne kasashen Sin da Zambiya suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya kan fitar da kwarurun macadamia nuts zuwa kasar Sin.
Bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar ya samu halarcin mukaddashin jakada na ofishin jakadancin Sin da ke Zambiya Wang Sheng, da ministan noma na kasar Zambiya Mtolo Phiri.
Kano Pillars Ta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Kocinta, Usman Abdallah Farashin Man Fetur Ya Ƙara Tashi Sakamakon Rikicin Dangote Da NNPCLA jawabinsa, Wang ya bayyana cewa, rattaba hannu kan yarjejeniyar ya kasance wani babban mataki na bude kasuwar kasar Sin ga kwayoyi dangin gyada na kasar Zambiya, wanda zai amfanar da manoman kasar nan gaba ba da jimawa ba. Ya kara da cewa, baya ga wannan yarjejeniyar da wata ta daban da aka cimma a baya kan fitar da ‘ya’yan itace na blueberry daga Zambiya zuwa kasar Sin, ana kuma ci gaba da shawarwarin fitar da sauran kayayyakin amfanin gona, kamar busasshen paprika da avocado zuwa kasar ta Sin.
Yarjejeniyar dai wani muhimmin sakamako ne na taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka da aka gudanar a birnin Beijing a watan Satumban bara, lokacin da kasar Sin ta bayyana kudurinta na soke haraji kashi 100 bisa 100 kan kayayyakin dukkan kasashe masu karancin ci gaba, wadanda take da huldar diflomasiyya da su, ciki har da kasar Zambiya. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp