Rahotanni na cewa Allah Ya yi wa Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sunusi ya rasuwa.
Wata sanarwa da ta fito daga cikin iyalansa ta tabbatar da rasuwar, inda ta ce nan gaba za a bayyana lokacin da za a yi masa jana’iza.
Alhaji Abbas Sanusi kawu ne ga Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II, kuma mahaifi ga shugaban jam’iyyar APC na Kano, Alhaji Abdullahi Abbas.
Marigayin shi ne Wamban Kano babban ɗan majalisar Sarki kafin daga likafar sarautarsa zuwa Galadiman Kano.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Jikamshi Zai Jagoranci Tsofaffin Ma’aikatan FRCN Zuwa PTAD Don Neman Biyan Haƙƙoƙi
Shugaban Ƙungiyar Tsofaffin Ma’aikatan FRCN, Alhaji Ibrahim Ahmad Jikamshi, zai jagoranci wata tawaga ta musamman domin ganawa da Babban Sakataren Hukumar PTAD kan muhimman batutuwa fansho da ta shafi tsofaffin ma’aikatan.
Alhaji Ibrahim Jikamshi dayake bayani a Kaduna, yace za a gudanar da wannan ganawa a cikin wannan mako domin tattaunawa kan wasu matsaloli da aka gano wajen biyan bashin da ake bin tsofaffin ma’aikatan shekaru da dama.
Ya tabbatar da cewa ƙungiyar tana ƙoƙari wajen shawo kan irin waɗannan matsaloli da suka dade ana fama da su, tare da fatan cewa hukumar PTAD za ta nuna gaskiya, rikon amana da kuma jajircewa wajen biyan hakkokin da suka rage.
Alhaji Ibrahim Jikamshi, wanda ya tunatar da matakin da shugaban ƙasa ya ɗauka a baya na biyan bashin da ake bin tsofaffin ma’aikata ta hanyar sakin biliyoyin Naira, ya nuna damuwa da cewa har yanzu wannan mataki bai haifar da gamsasshen sakamako ba ga waɗanda abin ya shafa.
SULEIMAN KAURA