Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tarayyar Najeriya ya tube shugaban kamfanin man fetur ta kasa NNPC Mele Kyari, da majalisar gudanarwansa, ya kuma maye gurbinsa ta

Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto kakakin fadar shugaban kasa Bayo Onanuga a safiyar yau Asabar a shafinsa X.

Onanuga shugaba ya tube shugaban kamfanin na NNPC da majalisar gudanarwan sa wadanda aka nada su a cikin watan Nuwamban shekara ta 2023.

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Kyara a matsayin shugaban kamfanin sannan ya sake nada shi a shekara ta 2023.

Banda haka shugaba Tinubu ya nada Engineer Bashir Bayo Ojulari, a matsayin sabon shugaban kamfanin sannan da wasu yan majalisar gudanarwa 11. Sannan majalisar tana da Ahmadu Musa Kida a matsayin mataimakin shugaban kamfanin.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Iran ta gargadi Amurka kan barazanar harin bam da Trump ya yi

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta gayyaci mai kula da harkokin kasar Switzerland da ke Tehran domin nuna fishi kan irin munanan ayyukan Isra’ila a yankin da kuma barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ke yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Babban daraktan ma’aikatar harkokin wajen Iran Issa Kameli ne ya gayyaci jami’in diflomasiyyar na Switzerland, wanda kasarsa ke wakiltar muradun Washington a Tehran, yau Litinin.

Kameli ya mika gargadin na Iran a hukumance ga wakilin kasar Switzerland dangane da duk wani aiki na barna tare da bayyana aniyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na mayar da kakkausan martani cikin tsauri kan duk wata barazana.

Jami’in diflomasiyyar na Iran yayi tir da kalaman tunzura tashe-tashen hankula wandanda kuma suka sabawa dokokin kasa da kasa da kuma tsarin Majalisar Dinkin Duniya.

Wakilin na Switzerland ya ba da tabbacin cewa nan take zai isar da sakon Iran ga gwamnatin Amurka.

A ranar Asabar ne Trump ya ce za a kai wa Iran hari idan ba ta kulla yarjejeniya da Amurka ba.

“Idan ba su kulla yarjejeniya ba, za a ji bama-bamai,” in ji shi a wata hira da NBC News. Ya kuma yi barazanar ladabtar da Iran.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansu
  • Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi
  • Tinubu ya cire Mele Kyari daga shugabancin NNPC
  • Ana Zaman Dar-dar A Kasar Zimbabwe Saboda Shirin Zanga-zangar Tsofaffin Sojaji
  • Mene ne matsayin azumin Sitta Shawwal a Mazhabar Malikiyya
  • NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Za Su Kwaɗaita Muku Azumtar Sitta Shawwal
  • Iran ta gargadi Amurka kan barazanar harin bam da Trump ya yi
  • Sani Ahmad Lere Na Radio Nijeriya Kaduna Ya Zama Falakin Lere
  • NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Komawa Cin Abinci Yadda Ya Kamata Bayan Watan Ramadana