Iran: Larijani Ya Ce Iran Zata Fara Kera Makaman Nukliya Idan An Kai Mata Hari Kan Shirin Ta Na Makamashin Nuliya
Published: 2nd, April 2025 GMT
Babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci Dr Ali Larijani, ya ce duk tare da cewa jagoran juyi juya halin musulunci ya bada fatawar hana kera makaman nukliya, amma idan an kaiwa kasar Iran hari kan shirinta na makamashin nukliya, wannan yana iya tunzura kasar ta kai ga mallakar makaman Nukliya.
Jaridar Tehran time ta nakalto Dr Larijani ya kara da cewa idan Amurka ko HKI ko duka biyu suka kaiwa cibiyoyin nukliyar kasar, to kuwa zata kera makaman nukliya.
A ranar Lahadin da ta gabata ce, Dr Larijani ya bayyana haka. Sai dai a daren Litinin ne Dr Larijani ta kara jaddada wannan matakin.
Sai dai kafin haka shugaban ma’aikatar leken asiri na Amurka ta tabbatarwa tashar talabijin ta NBC kan cewa Iran bata da shirin samar da makaman Nukliya.
Amma Trump ya sha nanatawa cewa iran Iran bata zo suka tattauna batun shirinta na makamashin nukliya ba sai ya kai hare-hare kan ciboyoyin makamashin nukliya na kasar Iran.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: makaman nukliya
এছাড়াও পড়ুন:
Arakci: Abokan Gaba Za Su Yi Nadamar Yi Wa Iran Barazana
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Arakci ya bayyana cewa, duk wata barazana da za a yi wa Iran za ta sa makiya su yi babbar nadama.
A wata hira a tashar talabijin din almasirah ta kasar Yemen ta yi da shi, ministan harkokin wajen na Iran ya ce, farfagandar da ake yi ta cewa, kai wa kasar Yemen hari share fage ne na yaki da Iran ba sabon abu ba ne, an sha yin irin wannan barazanar a baya.
Abbas Arakci ya kara da cewa; Iran ba za ta taba kyale duk wani mahaluki da zai rika yin Magana da ita da harshe na barazana ba, sannan ya kara da cewa makiya za su yi nadamar wannan barazanar.
Da yake Magana akan cigaba da kai wa Yemen hare-hare da Amurkan take yi, ministan harkokin wajen na Iran ya ce, nasarar da Yemen din take samu ne ya sa hakan take faruwa,kuma a cikin shekaru 10 na hare-haren da ake kai wa Yemen har yanzu an kasa yin galaba akan ta.