Aminiya:
2025-04-23@19:48:37 GMT

Muna samun galabar daƙile kwararowar baƙin haure — Jamus

Published: 2nd, April 2025 GMT

Gwamnatin Jamus ta ce tana ci gaba da samun galaba na daƙile kwararar baƙin haure masu shiga ƙasar tare da mayar da wadanda aka yi watsi da takardunsu na neman mafaka zuwa inda suka fito.

Ministar harkokin cikin gida ta Jamus, Nancy Faeser, ta bayyana cewa gwamnatin ƙasar mai barin gado ta taka muhimmiyar rawa wajen daƙile shigar baƙin haure cikin ƙasar.

Tinubu ya cire Mele Kyari daga shugabancin NNPC DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Arewa Ke Tafiya Kudu Farauta

Faeser ta ce gwamnatin na ci gaba da daukan matakin mayar da baƙin haure ƙasashen da suka fito, inda yanzu haka aka samu raguwar masu ajiye takardun neman mafaka a ƙasar, mafi ƙarfin tattalin arziki tsakanin ƙasashen Turai.

Faeser ta ce gwamnatin da Olaf Scholz ke jagoranta ta aiwatar da manufofi masu tasiri da suka taimaka wajen daƙile shigar baƙin haure zuwa ƙasar Jamus.

Nancy Faeser ’yar jam’iyyar SPD mai mulki za ta ajiye muƙamin na ministar cikin gida da zarar an kafa sabuwar gwamnati, bayan zaɓen da jam’iyyar CDU ta kasance a matsayi na farko wanda aka yi ranar 23 ga watan Fabrairun wannan shekara ta 2025.

Ana sa ran Friedrich Merz na jam’iyyar CDU ya zama shugaban gwamnatin na gaba da za a kafa a ƙasar ta Jamus.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Trump Na Shirin Rufe Ofisoshin Jakadanci A Afrika

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  WHO: Masu Ciwon Koda 400 A Gaza Sun Mutu Saboda Rashin Magani
  • Rage Mace-Macen Mata Da Jarirai: Kasar Sin Ta Ba Da Kyakkyawan Misali Ga Kasashe Masu Tasowa
  • Sabuwar Ƙungiyar ‘Yan Bindiga Ta Addabi Jihohin Kwara Da Neja
  • An daƙile yunƙurin juyin mulki a Burkina Faso
  • Rashin Tsaro: Gwamnatin Neja Ta Saka Dokar Zama A Gida A Minna
  • Sojoji Sun Daƙile Harin Boko Haram A Yobe
  • Burnley Da Leeds United Sun Dawo Gasar Firimiya Lig 
  • Sharhin Bayan labarai: Rage Kasafin Kudin Ma’ailatar harkokin wajen Amurka da tasirinsa
  • Sin Na Hasashen Samun Karin Yabanya A Shekarar 2025
  • Gwamnatin Trump Na Shirin Rufe Ofisoshin Jakadanci A Afrika