Kisan Mafarauta: Babu wanda aka kai wa harin ramuwar gayya a Kano — Ƙungiyoyin Matasa
Published: 2nd, April 2025 GMT
Ƙungiyar matasan Arewa ta yi Allah-wadai da jita-jitar da ake yaɗawa cewa an kashe wani ɗan ƙabilar Ibo a Jihar Kano saboda kisan wasu Hausawa mafarauta da ɓatagari suka yi kwanan a Jihar Edo.
A wani taron manema labarai da gamayyar ƙungiyoyin matasa na ƙabilu daban-daban, ta ce abin takaici ne kisan da aka yi wa Hausawa kuma tana miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su.
Kazalika, ƙungiyoyin sun yaba wa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa koƙarinsa na tabbatar da zaman lafiya ya ci gaba da ɗorewa a jihar ta hanyar ɗaukar matakan gaggawa da kuma kwantar da hankalin al’ummar Kano.
Haka kuma, shugaban ƙungiyar Nworisa Micheal, ya yi watsi da zancen da ke yawo a soshiyal midiya cewa wasu matasa sun halaka wani dan ƙabilar Ibo ibo mai suna Peter Chukwudi Nwanosike, ɗan asalin garin Abagana da ke Anambra mazauni a Kano, a matsayin martani kan kisan mafarautan.
“Saɓanin abin da ake yaɗawa ba kashe shi aka yi ba, tsautsayin masu ƙwacen waya ne ya afka kuma ya yi ƙoƙarin tserewa. Babu wanda ya caka masa makami kamar yadda ake yaɗawa.”
Ƙungiyoyin sun kuma gargaɗi kafafen yaɗa labari kan illar watsa labarai ba tare da bincike ba.
Kazalika sun yaba wa Sarkin Edo kuma Enogie II, Fred Edozele Akhigbe (JP), kan fitar da sanarwar yin tir da lamarin da ya faru a Edon sa’o’i kaɗan bayan faruwarsa, da gwamnan jihar, Monday Okpebholo, kan ziyarar jajen da ya kawo Kano, da kuma ƙoƙarinsa na samar da haɗin kai da adalci kan waɗanda lamarin ya rutsa da su.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan fashi sun kashe magidanci a Kano
Ana fargabar cewa wasu da ake zargin ’yan fashi ne sun kashe wani magidanci a unguwar Ɗanbare da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano.
Bayanai sun ce waɗanda ake zargin sun kashe magidancin ne da adda, bayan sun shiga gidansa da yake zaune domin sata da asuba.
To sai dai mazauna unguwar sun bayyana wa Aminiya cewa sun samu nasarar kama wanda suke zargin shugaban ’yan fashin ne, sun kuma miƙa shi ofishin ’yan sanda na Ɗorayi.