Tinubu Ya Tafi Faransa Ziyarar Aiki Na Mako 2
Published: 2nd, April 2025 GMT
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bar Abuja a yau Laraba zuwa Paris, na ƙasar Faransa, domin ziyarar aiki ta makonni biyu.
A cewar mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, Shugaba Tinubu zai yi bitar mulkinsa na rabin wa’adi, inda zai tantance nasarorin da ya cimma da kuma irin sauye-sauyen da yake aiwatarwa.
Sanarwar ta ce wannan lokaci zai ba shi damar tsara hanyoyin da za su inganta ci gaban ƙasa yayin da yake shirin cika shekaru biyu a kan mulki.
Duk da kasancewarsa a waje, Onanuga ya tabbatar da cewa Shugaba Tinubu zai ci gaba da gudanar da harkokin gwamnati tare da tuntuɓar manyan jami’ansa har zuwa lokacin da zai dawo gida.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Faransa gwamnati Paris Ziyara
এছাড়াও পড়ুন:
YANZU-YANZU: Gwamnan Edo Ya Kai Ziyarar Jaje Kan Kisan Mafarauta A Uromi
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp