Aminiya:
2025-04-08@04:41:06 GMT

Mutum 2 sun rasu, 13 sun ɓace a hatsarin jirgin ruwa a Bayelsa

Published: 2nd, April 2025 GMT

Mutum biyu sun rasa rayukansu, yayin da ake ci gaba da neman wasu mutum 13 da suka ɓace yayin wani hatsarin jirgin ruwa a Jihar Bayelsa.

Hatsarin ya faru ne da yammacin ranar Talata, lokacin da jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji ya yi karo da wani jirgin kamun kifi.

HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman Kano Muna samun galabar daƙile kwararowar baƙin haure — Jamus

Masu nutso a ruwa sun fara ƙoƙarin ceto waɗanda suka ɓace.

Bayanai sun nuna cewar wani jirgi mai suna ‘Meeting Marine’ wanda ya taso daga Anyama Ijaw zuwa Lubia da Foropa ya yi karo da jirgin kamun kifi.

Jirgin na da injin 115HP kuma wani mutum da ake kira Saturday ne yake tuƙa shi.

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan ruwa a Bayelsa, Kwamared Ogoniba Ipigansi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa har yanzu ba a samo mutum 13 ba.

Ya ƙara da cewa matsalar rashin ingantaccen yanayin sadarwa a yankin na hana aikin ceto tafiya yadda ya kamata.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Bayelsa, DSP Musa Muhammad, ya ce ba a kai musu rahoton faruwar lamarin ba tukuna, amma sun fara bincike.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Bayelsa Hatsarin Jirgin Ruwa

এছাড়াও পড়ুন:

Wani Kusa A Kungiyar Hamas Ya Yi Shahada A Wani Harin Isra’ila A Kudancin Lebanon

An kashe wani kusa a kungiyar  Hamas Hassan Farhat, wanda aka fi sani da Abu Yasser, da wasu mutane biyu a wani hari da jiragen yakin Isra’ila suka kai a wani gida a birnin Sidon, dake kudancin kasar Lebanon, a safiyar jiya Juma’a.

A cewar Al-Mayadeen, gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai wani hari ta sama kan wani gida da ke birnin Sidon da ke kudancin kasar Lebanon, inda harin ya kashe babban kusa na  Hamas Hassan Farhat da wasu mutane biyu daga cikin iyalansa.

A cewar rahoton, sojojin mamaya na Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun kai hari a Al-Naqoura, Nabatiyeh, da Sidon a kudancin kasar Lebanon a yammacin ranar Alhamis, inda suka yi barna a yankunan da aka kai harin.

Shafin tashar “Russia Today” ya bayar da labarin cewa: Bisa kididdigar farko da aka yi, “Hassan Farhat, wanda aka fi sani da Abu Yasser”, shugaban kusa a kungiyar Hamas, da dansa da ‘yarsa ne suka yi shahada a wani hari da jiragen Isra’ila suka kai a wani gida a yankin Dala’a a tsakiyar garin na Sidon. A wannan harin da aka kai ta hanyar amfani da jirgi maras matuki, an harba makamai masu linzami guda biyu a gidan.

Kawo yanzu kungiyar Hamas ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance game da shahadar Farhat ba, inda ta jaddada matsayinta na ci gaba da bin tafarkin neman ‘yanci wanda Farhat da iyalansa suka yi shahada a kansa.

Dangane da haka ne ma’aikatar lafiya ta kasar Labanon ta sanar a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu  wasu biyu kuma suka jikkata sakamakon wannan hari da jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a birnin da ke kudancin kasar Lebanon.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 30 a Kongo
  • Mutane 2 Sun Yi Shahada A Wani Hari Da Jirgin Sama Maras Matuki Na HKI Ya Kai Wa Kasar Lebanon
  • Ambaliya Ta Hallaka Mutum 30 A Birnin Kinshasa Na Jamhuriyar Demokradiyar Congo
  • Harin Filato: An kashe Mutane 40, An Kona Gidaje 383, Fiye Da Mutane 1,000 An Raba Su Da Muhallansu 
  • Mutanen da Sanƙarau ta kashe sun kai 151 — NCDC
  • Fasinja ya yi ƙoƙarin buɗe ƙofar jirgi a sararin samaniya
  • Ana Ci Gaba Da Kai Ruwa Rana Takanin Amurka Da China Kan Batun Harajin Fito
  • An kai wa motar haya hari an kashe mutum 2 da sace wasu a Benuwe
  • An ceto fasinjoji 14 a hannun ’yan bindiga, 3 sun rasu a Benuwe
  • Wani Kusa A Kungiyar Hamas Ya Yi Shahada A Wani Harin Isra’ila A Kudancin Lebanon