Uromi: Barau ya ziyarci iyalan waɗanda aka kashe, ya ba su kyautar N16m
Published: 2nd, April 2025 GMT
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, ya ziyarci iyalan mafarauta 16 da aka kashe a yankin Uromi da ke Jihar Edo, tare da ba su tallafin Naira miliyan 16.
Matan matatan sun fito ne daga ƙananan hukumomin Bunkure, Kibiya, Rano, da Garko a Jihar Kano.
Mutum 2 sun rasu, 13 sun ɓace a hatsarin jirgin ruwa a Bayelsa HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman KanoBarau ya gana da iyalan mamatan a Masallacin At-Taqwa da ke Bunkure a ranar Laraba tare da Ministan Harkokin Gidaje, Yusuf Abdullahi Ata da sauran manyan jami’ai.
Barau, ya yi ta’aziyya da kuma tabbatar da cewa waɗanda suka aikata laifin za su fuskanci hukunci.
“Na zo nan ne domin na taya ku jaje kan wannan mummunan al’amari da ya jawo rasuwar ’yan uwanku 16 a ranar Alhamis da ta gabata.
“Allah Ya Aljanna Firdausi ta zama makomarsu, Ya bai wa waɗanda suka ji rauni lafiya,” in ji Barau.
“Ba za mu ɗauki hakan da sauƙi ba. Za mu tabbatar cewa waɗanda suka aikata laifin za su fuskanci hukunci.”
Barau, ya kuma sanar da bai wa kowane daga cikin iyalan mamatan kyautar Naira miliyan ɗaya, wanda ya kai jimillar Naira miliyan 16.
Da yake magana a madadin iyalan mamatan, Sheikh Zainul Abidina Auwal, limamin yankin, ya gode wa Barau bisa ƙoƙarinsa da yadda ya damu da lamarin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: iyalai mafarauta Sanata Barau
এছাড়াও পড়ুন:
Wani Harin Amurka kan Yemen ya kashe fararen hula akalla 12
Amurka ta sake kai wani hari ta sama kan babban birnin kasar Yemen, Sana’a, inda ta kashe fararen hula akalla 12 tare da jikkata wasu fiye da 30 na daban.
Mummunan harin na Amurka an kai shi ne a wata kasuwa mai cike da cunkoson jama’a a unguwar al-Farwa da ke gundumar Sha’ub a safiyar ranar Litinin.
Ana fargabar adadin wadanda suka mutu zai karu yayin da mutane da dama ke makale a karkashin baraguzan gine-gine da aka wargaza a harin.
A gefe guda kuma, Amurka ta kai hare-hare a yankunan lardin Sa’ada, a arewa mai nisa na kasar, da tsakiyar Ma’rib, da yammacin Hudaydah.
Dama kafin hakan a ranar Lahadi, Amurka ta kai wasu hare-hare ta sama a Yemen, ciki har da Sana’a, inda aka kashe akalla uku.
A cikin watan da ya gabata ne dai sojojin Amurka suka zazafa kai hare-hare a kasar Yemen, bisa ikirarin dakile hare-haren kungiyar Ansarullah dake kai farmakin goya bayan falasdinu kan jiragen ruwa masu alaka da Isra’ila.
Fiye da mutane 200 ne aka kashe a harin da Amurka ta kai kan Yemen tun cikin watan Maris.