Araghchi : Iran a shirye take don tattaunawa amma barazanar soji daga Amurka na dagula yanayin’
Published: 2nd, April 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya nanata shirin Tehran na shiga tattaunawar da Amurka kan shirinta na nukiliya na zaman lafiya, yana mai gargadin cewa barazanar soji daga Amurka na dagula halin da ake ciki a yanzu.
“Jamhuriyar Musulunci, kamar yadda ta kasance a baya, a shirye take don yin shawarwari na hakika,” in ji Araghchi a wata wayar tarho da takwaransa na Holland, Caspar Veldkamp, yau Laraba.
Ya jaddada cewa wannan “yana bukatar yanayi mai kyau da kuma nisantar hanyoyin da suka shafi barazana.”
Ministan ya yi Allah wadai da barazanar da jami’an Amurka suka yi wa Iran da cewa “ba za a amince da su ba”, ya kara da cewa sun saba wa kundin tsarin mulkin MDD da dokokin kasa da kasa, hasali ma suna “rikitar” halin da ake ciki.
Araghchi ya yi gargadin cewa Iran za ta mayar da martani “cikin gaggwa” ga duk wani cin zarafi a kan iyakokinta, huruminta, da kuma muradun kasarta.
A halin da ake ciki kuma, ya soki kungiyar Tarayyar Turai kan gazawarta na daukar matsaya kan kalaman na jami’an Amurka, wadanda ya ce suna barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa.
A nasa bangaren, Veldkamp ya bayyana damuwarsa game da karuwar tashe-tashen hankula a yankin, yana mai jaddada bukatar hanyoyin diflomasiyya wajen warware takaddamar.
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar a karshen mako cewa zai iya ba da umarnin kai hare-haren soji kan Iran idan Tehran ta ki shiga tattaunawa don “saka sabuwar yarjejeniya” kan shirinta na nukiliya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Trump Ya Ƙaƙaba Wa Nijeriya Da Ƙasashen Duniya Haraji
Harajin kan motocin da ake shigo da su Amurka daga ƙasashen waje zai kai 25, wanda zai fara aiki daga ƙarfe 12 na daren ranar Laraba.
Shugaba Trump ya ce matakin na nufin kare tattalin arziƙin Amurka da muradun ‘yan ƙasarta.
Ana sa ran ƙasashe kamar Tarayyar Turai, China, Japan, da Koriya ta Kudu za su mayar da martani cikin gaggawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp