HausaTv:
2025-04-03@14:33:21 GMT

Isra’ila na karbe yankuna a zirin Gaza

Published: 2nd, April 2025 GMT

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa sojojin kasar na karbe iko da wasu yankunan zirin Gaza, a wani mataki na kara matsin lamba kan kungiyar Hamas domin tilasta ta sakin mutanen da ta ke garkuwa da su.

“Muna karbe zirin Gaza tare da kara matsin lamba mataki-mataki domin tilasta su mayar da mutanen da aka yi garkuwa da su,”inji  Netanyahu a wani faifan bidiyo da ofishinsa ya fitar.

Ya kara da cewa, Sojoji na karbe yankuna, suna kai farmaki kan ‘yan wadanda ya danganta da ‘yan ta’adda in ji shi, yana mai sanar da samar da wata sabuwar hanya karkashin ikon Isra’ila don raba garuruwan Khan Younis da Rafah (kudu).

Tunda farko dama ministan tsaron Isra’ila Israel Katz ya sanar a Larabar nan cewa, kasarsa ta fadada kaddamar da hare-haren soji a sassan zirin Gaza, yana mai barazanar dakarun Isra’ila za su kwace karin yankuna a zirin da nufin samar da yankuna masu tsaro da za su raba Isra’ila da wurare masu fama da tashin hankali.

Cikin wata sanarwa, mista Katz ya ce matakin fadada ayyukan sojin zai kunshi fadada kwashe mutane daga yankunan da ake dauki ba dadi a Gaza.

Isra’ila dai ta kawo karshen wa’adin tsagaita wuta na watanni 2 tun a ranar 18 ga watan Maris da ya shude, inda ta koma kaddamar da munanan hare-hare ta sama da kasa kan wuraren da Falasdinawa ke fakewa.

A jiya Talata, hukumomin lafiya a Gaza sun ce kawo yanzu sabbin hare-haren sun sabbaba rasuwar Falasdinawa 1,042 tare da jikkata wasu 2,542, yayin da rikicin da ya barke tun daga watan Oktoban shekarar 2023 zuwa yanzu, ya haddasa jimillar asarar rayukan Falasdinawa 50,399, tare da jikkata wasu 114,583.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

 Larijani:  Dole Iran Ta Kera Makaman Nukiliya Idan Amurka Da Isra’ila Su Ka Kawo Ma Ta Hari

Mai bai wa jagoran juyin musulunci na Iran shawara Dr. Ali Larijani ya ce, idan har Amurka da Isra’ila su ka fake da batun shirin makamashin Nukiliyar Iran na zaman lafiya, su ka kawo mata hari, to ya zama wajibi a gare ta ta kera makaman Nukiliya.

Dr. Ali Larijani wanda tashar talabijin din Iran ta yi jira da shi a jiya Litinin da dare, ya bayyana cewa; manyan kasashen duniya suna son yin alaka kai tsare da Iran cikin ‘yanci, sai dai suna da fuskantar matsin lamba daga Amurka.

Tsohon shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran ya kuma kara da cewa; Idan har Amruka da HKI su ka kawo wa Iran hari, to, za ta dau hanyar kera makaman Nukiliya, kuma su kansu al’ummar kasa abinda za su so ganin ya faru kenan.

Dr. Ali Larijani wanda memba ne a cikin majalisar fayyace maslahar tsaron musulunci, ya kara da cewa; Yaki da Iran ba abu ne mai sauki ba, yana da tattare da hatsarin da zai koma kan mahara.

Larijani ya kuma ce; Fatawar Jagora ita ce, ta haramta mallakar makamin Nukiliya,amma idan Amurka ta yi kuskure, to matsin lambar mutane zai sa Iran ta kama hanyar kera makaman Nukiliya.

Har ila yau, Larijani ya ce; Fasahar Nukiliya da Iran take da ita, an tsara ta akan cewa, ko da an kawo wa Iran din hare-hare, to za ta ci gaba da aiki ba tare da tsaiko ba. Kum su kansu masu hankali daga cikin makiya sun san cewa idan su ka kawo wa Iran farmaki, to kuwa za ta daura damarar kera makaman Nukiliya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ƙoƙarin Tsige Sanata Natasha Ya Gaza Cika Ƙa’idar Doka – INEC
  • Sabbin Hare-Haren Jiragen Yakin Amurka A Kan Kasar Yemen Ya Jawo Rasa Karin Rayuka A kasar
  • Yau Ce Rana Mafi Muni A Gaza A Cikin Makonni Biyu
  • Rundunar PLA Ta Kaddamar Da Atisaye A Yankunan Tsakiya Da Kudancin Zirin Taiwan 
  • ICC ta yi kakkausar suka ga Hungary saboda yin watsi da sammacin kama Netanyahu
  • Isra’ila ta kashe yara 322 cikin kwanaki 10 a Gaza — UNICEF
  •  Larijani:  Dole Iran Ta Kera Makaman Nukiliya Idan Amurka Da Isra’ila Su Ka Kawo Ma Ta Hari
  • Arakci: Abokan Gaba Za Su Yi Nadamar Yi Wa Iran Barazana
  • Gaza : Fiye da mutane 1,000 Isra’ila ta kashe tun daga ranar 18 ga Maris