A ranar Talata ne, Allah ya yi wa Alhaji Abbas Sanusi, Galadiman Kano kuma babban mai nada sarki a masarautar Kano rasuwa. A safiyar Laraba, 2 ga watan Afrilun 2025 aka yi jana’izar sarkin wanda ya shafe fiye da shekaru 60 yana hidimtawa masarauta, ya rasu yana da shekara 92 bayan doguwar jinya. Ya bar ‘ya’ya da jikoki da dama.

Mu Leka Shirin “Bunkasa Tagomashin Kirkirarriyar Basira Ta AI” Na Kasar Sin Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi Daga cikin ‘ya’yansa akwai Alhaji Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano. Kano, jiha ce da hamayyar siyasa da rikicin masarauta ya dabaibaye ta. Akwai hamayyar siyasa tsakanin shugabannin jam’iyyun NNPP mai mulki a jihar da takwararta ta APC wacce Abdullahi Abbas kuma ɗa ga Galadima ke shugabanta a jihar. A ɓangaren Masarauta, Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya tumɓuke Sarki Aminu Ado Bayero inda ya maye gurbinsa da Sarki Sanusi II, wanda yanzu haka suke gaban kotu. Jana’izar Galadima da aka yi a fadar Kano, kofar kudu, ta hada kawunan duka bangarorin da ke hamayya da juna a jihar. Jiga-jigan Jam’iyyar NNPP a jihar da suka hada da shugabanta na Kasa, Engr. Rabiu Musa Kwankwaso, gwamna Abba Kabir Yusuf da sauransu duk sun halarci jana’izar yayin da a ɓangaren APC, Akwai shugaban jam’iyyar, Abdullahi Abbas, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin da sauransu. Sai dai, Sarki Aminu Ado Bayero bai samu halartar jana’izar ba duba da yanayin tsaro.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Janar Tsiga Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Bayan Shafe Kwanaki 56 A Hannun ‘Yan Bindiga 

Wani makusancin dangin Janar tsiga, ya shaida wa Daily trust cewa, bayan sun karbi kudin, masu garkuwa da mutanen sun ajiye Tsiga har tsawon mako guda kafin su tuntubi iyalan shi, inda daga bisani suka hada Janar din da ‘yan uwanshi a waya domin tattaunawa da su.

 

Ya kara da cewa, masu garkuwa da mutanen sun bukaci a kara musu kudin fansa, amma hakan ba ta yi wu ba.

 

Wata majiya mai tushe ta sojoji ta kuma tabbatar da sakin Tsiga. Majiyoyi na kusa da dangin sun ce yana cikin koshin lafiya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Janar Tsiga Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Bayan Shafe Kwanaki 56 A Hannun ‘Yan Bindiga 
  • Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi
  • Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi
  • HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman Kano
  • Allah Ya Yi Wa Galadiman Kano, Abbas Sanusi, Rasuwa 
  • Galadiman Kano Abbas Sunusi ya rasu
  • Sarki Sanusi Ya Yabawa Gwamna Yusuf Kan Manufofin Habaka Jama’ar Kano
  • HOTUNA: Sarki Sanusi ya kai wa Abba ziyarar barka da Sallah
  • HOTUNA: Sarki Sanusi ya kai wa Gwamna Abba ziyarar barka da Sallah