Janar Tsiga ya kuɓuta bayan shafe kwana 56 a hannun ’yan bindiga
Published: 3rd, April 2025 GMT
Birgediya-Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya), ya kuɓuta bayan shafe kwana 56 a hannun ’yan bindiga.
An sace Janar Tsiga, wanda Tsohon Shugaban Hukumar NYSC ne, a garinsu da ke Ƙaramar Hukumar Bakori a Jihar Katsina, a ranar 5 ga watan Fabrairu, 2025.
Mutum ɗaya ya rasu, 3 sun jikkata a rikicin ’yan sara-suka a Filato HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman KanoHakazalika, aharan sun sace mutum tara a tare da shi a lokacin da suka kai harin.
Duk da cewa iyalansa sun biya kuɗin fansa, ’yan bindigar sun ci gaba da tsare shi na tsawon makonni.
Rahotanni sun nuna cewa har yanzu ba a san adadin kuɗin da aka biya a matsayin kuɗin fansar ba.
Wasu sun ce Naira miliyan 60 aka biya, amma wasu majiyoyi masu tushe sun ce an biya sama da haka.
Wani daga cikin iyalansa ya bayyana cewa bayan maharan sun karɓi kuɗin, sai suka yi shiru har na tsawon mako guda, kafin daga bisani su kira iyalansa a ranar 11 ga watan Maris, inda suka ba shi ya yi magana da su.
Daga baya, sun sake neman ƙarin kuɗi, amma iyalan nasa ba su ƙara musu ba.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa yanzu haka yana Jihar Zamfara, wanda daga nan za a kai shi Abuja.
Wani jami’in soja ya tabbatar da sakinsa, inda ya ce yana cikin ƙoshin lafiya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga hari Janar Tsiga
এছাড়াও পড়ুন:
Yawan Falasdinawan Da Suka Yi Shahada Sakamakon Hare-Haren ‘Yan Sahayoniyya Sun Kai 51,266
Adadin Falasdinawa da suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da irin sojojin mamayar Isra’ila kan Gaza ya kai shahidai 51,266
Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa: An isar da gawawwakin shahidai 26 da kuma wasu 60 da suka jikkata a asibitocin zirin Gaza cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
Ma’aikatar ta bayyana a cikin wata sanarwa a jiya Talata cewa adadin wadanda suka yi shahada da wadanda suka jikkata tun ranar 18 ga Maris, shekara ta 2025 ya kai shahidai 1,890 da kuma jikkata wasu 4,950 na daban.
An tabbatar da cewa adadin wadanda suka yi shahada a sakamakon harin ta’addancin ‘yan sahayoniyya ya karu zuwa shahidai 51,266 da jikkatan wasu 116,991 tun daga ranar 7 ga Oktoban shekara ta 2023.