Janar Tsiga Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Bayan Shafe Kwanaki 56 A Hannun ‘Yan Bindiga
Published: 3rd, April 2025 GMT
Wani makusancin dangin Janar tsiga, ya shaida wa Daily trust cewa, bayan sun karbi kudin, masu garkuwa da mutanen sun ajiye Tsiga har tsawon mako guda kafin su tuntubi iyalan shi, inda daga bisani suka hada Janar din da ‘yan uwanshi a waya domin tattaunawa da su.
Ya kara da cewa, masu garkuwa da mutanen sun bukaci a kara musu kudin fansa, amma hakan ba ta yi wu ba.
Wata majiya mai tushe ta sojoji ta kuma tabbatar da sakin Tsiga. Majiyoyi na kusa da dangin sun ce yana cikin koshin lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Iran ta mayar wa Amurka martani kan barazanar kai mata hari
Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya yi kakkausan gargaɗi kan barazanar Amurka da ƙawayenta na kai wa ƙasarsa hari.
Khamenei ya sha alwashin maida mummunar martani idan har Amurka da ƙaddamar da hare-hare a ƙasar ta Iran.
Gargaɗin nasa martani ne kan barazanar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa ƙasar cewa za su kai mata hari.
Muna jiran ganin hukuncin da za a ɗauka kan kashe ’yan Arewa a Edo — Sarkin Musulmi Kisan Mafarauta: Matakan da gwamnatin Edo da ta Kano suke ɗauka“Suna yi min barazana, kuma idan suka sake suka kawo min hari tabbas zan rama,” in ji shi.
Yayin wata tattaunawa a ranar Asabar ne Trump ya yi alƙawarin kai wa Iran ɗin hari matuƙar ba ta amince da yarjejeniyar makamin ƙare dangin ba.
“Idan ba su amince da sabuwar yarjejeniyar makaman ƙare dangin ba, za mu tada bama-bamai,” in ji Trump.
Sai dai bai bayyana ko Amurkan ce za ta kai harin ba ko kuma ƙawarta Isra’ila.
To sai dai cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin X, kakakin ma’aikatar wajen Iran Esmaeil Baqaei ya ce barazanar ta Trump a bainar duniya yana matsayin shugaban kasa abin mamaki ne, kuma babbar barazana ce ga zaman lafiya da tsaron ƙasa da ƙasa.