HausaTv:
2025-04-04@01:09:05 GMT

 Syria: Jiragen Yakin HKI Sun Kai Wa Birane Uku Na Kasar Syria Hari

Published: 3rd, April 2025 GMT

Da marecen jiya Laraba jiragen yakin HKI sun kai wasu jerin hare-hare akan biranen Damascus, Hums,  Dar’ada Humah.

Tashar Talabijin din ‘almayadin’ wai watsa shirye-shiryenta daga kasar Lebanon ta bayyana cewa; An kai harin ne akan wata cibiyar bincike a yankin Barzah dake arewacin birnin Damascus.

Wata majiyar asibiti ta shaida wa tashar talabijin din ta almayadin cewa, an sami wadanda su ka jikkata.

A garin Humah, jiragen yakin na HKI sun kai wasu hare-haren har sau 10, sannan kuma jiragen sun dauki lokaci mai tsawo suna shawagi a samaniyar birnin wanda ya yi sanadiyyar harin.

A birnin Hums, kafafen watsa labarun yankin sun ce an ji karar fashewar abubuwa masu karfin gaske a kusa da filin saukar jiragen sama na T4. Tashar talabijin din HKI ta 12, ta ce, filin saukar jiragen saman na T4 yana cikin wuraren da aka kai wa harin.

A wani gefen tankokin yakin HKI sun yi kutse cikin yankin Dar’a wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane da dama, da ya zuwa yanzu ba a tantance adadinsu ba.

 Tun a 1967 ne dai sojojin HKI su ka mamaye tuddan Gulan, a yanzu kuma bayan faduwar gwamnatin Basshar Asad tana ci gaba da kai wa kasar hare-hare.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Tarayyar Afirka Tana Shiga Tsakanin Bangarorin Dake  Rikici  Da Juna A Kasar Sudan Ta Kudu

 Wakilan kungiyar tarayyar Afirka sun isa birnin Juba na kasar Sudan ta Kudu, a kokarin da suke yi na shiga tsakanin hana komawa yakin basasa.

Tarayyar Afirkan ta fara kokarin shiga tsakani ne, bayan daurin talala da aka yi wa mataimakin shugaban kasa Riek Machar a gidansa,lamarin da ya sake jefa kasar cikin zaman dar-dar.

Gwamnatin Salva Kir tana zargin Machar da cewa yana rura wutar wani sabon yaki a cikin kasar. A ranar Laraba ta makon da ya shude ne dai aka yi wa mataimakin shugaban kasar daurin talala a gidansa saboda fadan da ake yi a yankin Upper Nile tsakanin sojojin gwamnati da kuma masu dauke da makamai na rundunar “White Army”.

A lokacin yakin basasar da kasar ta fuskanta a tsakanin 2013 zuwa 2018, an yi kawance a tsakanin mayakan “White Army” da kuma rundunar Machar, sai dai a wannan lokacin mataimakin shugaban kasar ya karyata cewa yana da alaka da abinda yake faruwa.

Tawagar tarayyar Afirkan da ta isa birnin Juba ta kunshi majalisar dattijan nahiyar Afirka, da ta kunshi tsohon shugaban kasar Burundu, Domitien Ndayizeye da kuma tsohon alkali daga kasar Kenta Effie Owuor.

A ranar Litinin din da ta gabata maid a tsohon shugaban kasar Kenya Fira ministan Kenya Raila Odinga ya isa birnin na Juba, a madadin kungiyar kasashen gabashin nahiyar Afirka.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dakarun Yemen Sun kai hari kan jirgin ruwan yaki na Amurka USS Harry Truman da makamai masu linzami
  • Bello Turji ya kashe manoma 11 a wani sabon hari a Sakkwato 
  • Sabbin Hare-Haren Jiragen Yakin Amurka A Kan Kasar Yemen Ya Jawo Rasa Karin Rayuka A kasar
  • Tarayyar Afirka Tana Shiga Tsakanin Bangarorin Dake  Rikici  Da Juna A Kasar Sudan Ta Kudu
  • Jiragen Yakin HKI Sun Kai Wa Kudancin Lebanon Hari Da Safiyar Yau Alhamis
  • Obasanjo Zai Zuba Jarin Dala Miliyan 700 A Kamaru
  • Wang Yi Ya Jinjina Wa Gudummawar Da Sinawa Da ’Yan Rasha Suka Bayar A Yakin Duniya Na Biyu
  • Sojojin Yemen Sun Harbo Jirgin Leken Asirin Amurka Samfurin MQ9
  • HKI Ta Sake Kai Wa Unguwar Dhajiya Dake Beirut Hari