HausaTv:
2025-04-04@02:30:55 GMT

Jiragen Yakin HKI Sun Kai Wa Kudancin Lebanon Hari Da Safiyar Yau Alhamis

Published: 3rd, April 2025 GMT

Rahotanni daga kasar Lebanon sun ce jiragen yakin HKI sun kai hari a garin “Naqura” dake kudancin Lebanon da safiyar yau Alhamis.

Jiragen yakin na ‘yan sahayoniya sun kai harin ne har sau uku ajere akan wata tsohuwar cibiyar kiwon lafiya dake cikin garin, haka nan kuma akan wasu gudajen mutane da suke a kusa.

Ya zuwa yanzu dai babu cikakken bayani akan asarar rayuka sanadiyyar wadannan hare-haren na’yan sahayoniya.

A shekaran jiya Talata ma dai sojojin na mamaya sun kai wa unguwar Dhahiya dake birnin Beirut hari wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane da dama da kuma jikkata wasu.

Hari na shekaran  jiya shi ne irinsa na biyu a cikin unguwar Dhahiya tun bayan tsagaita wutar yaki. Haka nan kuma suna ci gaba da kai wasu hare-haren a kudancin Lebanon daga lokaci zuwa lokaci.

Kungiyar Hizbullah ta yi gargadin cewa, ya zama wajibi ga gwamnatin kasar da ta yi amfani da dukkanin hanyoyin da take da su domin takawa ‘yan sahayoniyar birki, gabanin ita ta dauki matakin da ya dace.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Yau Ce Rana Mafi Muni A Gaza A Cikin Makonni Biyu

Sojojin HKI sun kashe akalla mutane 80 a asbitin Jabaliya a safiyar yau Alhamis, sannan sji ne hari mafi muni da ta kai kan gaza tun bayan da ta sake komawa yakin tufanul Aksa, makonni biyu da suka gabata.

Asbitin hukumar UNRWA ta MDD na daga cikin wuraren da yahudawan suka kai  hare-hare a garin a safiyar yau.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa Asbitin na daga cikin wuraren da HKI ta kaiwa hari a jiya Laraba inda. Sannan a safiyar yau ta kashe mutane akalla 22 a kan cikin asbitin kadai sannan daga ciki har da yara, da mata da kuma jami’an yansanda na gaza.

A jiya laraba kadai sojojin yahudawan sun kai hare-hare masu yawa a kan Khan Yunus, Rafah Nusairat da kuma tsakiyar Gaza.

Bayan hare-hare na safiyar yau Alhamis ne Sanata Bernie Sanders na majalisar dokokin kasar Amurka ya tura sakoa a shafinsa na Internet kan cewa zai gabatar da kuduri wanda zai hana gwamnatin kasar Amurya sayarwa HKI makamai wadanda yawansu ya kai dalar Amurka biliyon 8.8.

Tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 zuwa yanzu dai sojojin HKI sun kashe Falasdinawa akalla dubu 50, sannan ta raunata wasu kimani 112,000.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dakarun Yemen Sun kai hari kan jirgin ruwan yaki na Amurka USS Harry Truman da makamai masu linzami
  • Sabbin Hare-Haren Jiragen Yakin Amurka A Kan Kasar Yemen Ya Jawo Rasa Karin Rayuka A kasar
  • Yau Ce Rana Mafi Muni A Gaza A Cikin Makonni Biyu
  •  Kasar Afirka Ta Kudu Tana Ci Gaba Da Bibiyar “Isra’ila” A Kotun Duniya Ta Manyan Laifuka
  •  Syria: Jiragen Yakin HKI Sun Kai Wa Birane Uku Na Kasar Syria Hari
  • DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Arewa Ke Tafiya Kudu Farauta
  • Wang Yi Ya Jinjina Wa Gudummawar Da Sinawa Da ’Yan Rasha Suka Bayar A Yakin Duniya Na Biyu
  • Kungiyar “Amnesty” Na Zargi Netanyahu Da Aikata Laifukan Yaki
  • HKI Ta Sake Kai Wa Unguwar Dhajiya Dake Beirut Hari