Kasar Afirka Ta Kudu Tana Ci Gaba Da Bibiyar “Isra’ila” A Kotun Duniya Ta Manyan Laifuka
Published: 3rd, April 2025 GMT
Gwamnatin Afirka Ta Kudu ta sake jaddada azamarta ta bibiyar HKI a kotun duniya ta manyan laifuka akan laifukan kisan kiyashi da ta aikata a Gaza.
Gwamnatin ta Afirka ta kudu, ta kuma yi watsi da duk wani matsin lamba da Amurka yake yi ma ta domin tilasta ma ta, ta ja da baya.
Ministan alakar kasashen waje da aiki tare, Ronald Lamola wanda ya yi Magana da ‘yan jaridar kasar tasa, ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi kasar ta janye karar da ta shigar a gaban kotun kasa da kasa ta manyan laifuka.
Haka nan kuma ya ce; Neman yardar Amurka ba shi ne aikin da Afirka ta Kudu ta sanya a gaba ba, abinda yake gabanta shi ne tabbatar da adalci da kuma aiki da dokokin kasa da kasa.”
Lamola wanda yake halartar wani taro na MDD a birnin New york ya yi ishara da yadda kasarsa take fuskantar matsin lamba kai tsaye daga gwamnatin Amurka, amma duk da haka ba za ta janye ba, yana mai kara da cewa, manufarsu ita ce ganin an hukunta wadanda su ka aikata laifuka akan fararen hula a Gaza.
Lamola ya kuma ce, abinda suke yi ba wasan kwaikwayo ba ne ko siyasa, batu ne da yake da alaka da dokokin kasa da kasa.
A watan Disamba na 2023 ne dai kasar Afirka Ta Kudu kai karar HKI a gaban kotun kasa da kasa saboda laifukan yakin da take tafkawa akan al’ummar Falasdinu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Iran Ta Bayyana Cewa Kakaba Takunkumi Kan Kasarta Ya Sabawa Hikimar Gudanar Da Zaman Tattaunawa Da Ita
Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ta bayyana cewa; Kakaba takunkumi kan kasarta ya sabawa ikirarin Amurka na yin shawarwari da ita
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan matakin da Amurka ta dauka na kakabawa wasu gungun mutane masu alaka da bangaren makamashi, man fetur da iskar gas da kuma wasu mutane da dama masu fafutuka a shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na lumana takunkumi.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Baqa’i ya bayyana manufar takunkuman da Amurka ta kakabawa al’ummar Iran da cewa; A fili take nuna kyama ga masu yanke shawaran Amurka kan al’ummar Iran da kuma nuna rashin mutunta doka da hakkin dan Adam ne.
Ya kara da cewa: Dogaro da tsarin gwamnatocin Amurka da suka shude kan takunkumin tattalin arziki a kan kasashe masu tasowa, a matsayin makamin tsoratarwa da matsin lamba na siyasa, wani lamari ne da ya saba wa muhimman ka’idojin Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya da kuma dokokin kasa da kasa, kuma yana yin zagon kasa ga ginshikin doka da ka’idojin ciniki cikin ‘yanci, kuma yana haifar da keta hakkin bil’adama na asali na al’ummomin da takunkumin ya shafa, musamman ‘yancin ci gaba. Wannan hali sau da yawa yana zama laifi ga ɗan adam.