Matashi ya daɓa wa abokinsa wuƙa a kan budurwa
Published: 3rd, April 2025 GMT
Wani matashi mai shekaru 27, Rabiu Suleiman, ya daɓa wa abokinsa Yunusa Muazu wuƙa, tare da yi masa mummunan rauni, a kan budurwa a yankin Gwagwalada da ke Abuja.
Lamarin ya faru ne a daren Talata a wani gidan kallon fina-finai a Unguwar Dodo.
NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansu Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano, Abbas SanusiSuleiman ya zargi Muazu da yin soyayya da budurwarsa wadda yake shirin Jamila Yakubu.
Faɗan ya fara ne lokacin da Suleiman ya samu Jamila da Muazu suna tattaunawa a gidan kallon fina-finan.
Suleiman, ya fusata lokacin da ya ga Jamila tare da abokinsa, sai ya tafi kai-tsaye ya hau abokinsa da duka.
A lokacin da suke faɗa , Suleiman ya fito da wuƙa sannan ya daɓa wa Muazu a gadon baya.
Wannan abu ya ja hankalin wasu daga cikin mutanen da ke cikin gidan kallon, wanda hakan ya sa aka yi gaggawar kiran ’yan sanda, kuma nan take suka tafi da Suleiman.
An kai Muazu zuwa asibiti domin kula da shi.
Kakakin rundunar ’yan sandan birnin tarayya, SP Josephine Adeh, ba ta amsa kira da saƙonnin waya kan lamarin ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Faɗa Gwagwalada zargi
এছাড়াও পড়ুন:
Motar hatsi ta kashe masu bikin Ista 5 a Gombe
Hatsarin mota ya yi ajalin mutum biyar tare da jikkatar wasu takwas a yayin da suke bikin Ista a garin Billiri da ke Jihar Gombe.
Hatsarin ya faru ne a safiyar ranar Litinin, lokacin da direban wata babbar mota mai ɗauke da buhunan hatsi daga Jihar Adamawa ya auka kan dandazon jama’a da ke tsaka da shagalin bikin Ista.
An jingine wasanni a Italiya saboda mutuwar Fafaroma Francis An kama tsohuwa kan zargin lalata da almajiri a BauchiA wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun yi gaggawar kai ɗauki, inda suka kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibiti.
Sanarwar ta kuma ce bayan faruwar hatsarin, wasu fusatattun matasa sun cinna wa motar wuta tare da sace kayayyakin da ta ɗauko.
“Lokacin da ‘yan sanda suka kai ɗauki, matasan sun yi musu ruwan duwatsu, sai dai an shawo kan lamarin, kuma an dawo da zaman lafiya a yankin.”
Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Gombe, Bello Yahaya, ya bayyana jimami kan faruwar lamarin tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan mamatan.
Shi ma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bayyana damuwa kan wannan iftila’i.
A cikin wata sanarwa da Babban Daraktan yada labarai na gidan gwamnati, Isma’ila Uba Misilli ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa lamarin abu ne mai girgiza zuciya.
Gwamnatin jihar ta yi alƙawarin ɗaukar nauyin magani ga waɗanda suka ji raunuka, tare da tabbatar da cewa za a ɗauki matakan kare faruwar irin wannan matsala a nan gaba.