Najeriya ta yi kuskuren barin Boko Haram ta yi ƙarfi — Muftwang
Published: 3rd, April 2025 GMT
Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato, ya yi gargaɗin cewa Najeriya ta yi kuskure a baya wajen barin Boko Haram da sauran ƙungiyoyin ’yan bindiga har suka yi ƙarfi.
Ya jaddada cewa babu wata ƙungiya da ya kamata ta mallaki makamai ko ta samu ƙarfin guiwar ƙalubalantar hukumomin tsaro.
NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansu Uromi: Barau ya ziyarci iyalan waɗanda aka kashe, ya ba su kyautar N16mDa yake jawabi a Abuja yayin ƙaddamar da jiragen yaƙi marasa matuki da bama-baman da aka ƙera a Najeriya, wanda kamfanin Briech UAS ya samar, Mutfwang ya buƙaci haɗin gwiwa da kamfanonin fasahar tsaro na cikin gida.
“Dole ne mu tabbatar da cewa babu wata ƙungiya da ke iya ƙalubalantar hukumomin tsaronmu,” in ji Mutfwang.
“Najeriya ba za ta sake yin kuskuren barin ‘yan ta’adda su sake yin irin wannan ƙarfi ba.”
Ya yaba wa sojoji kan ƙoƙarinsu na inganta tsaro a Jihar Filato: “Saboda amfani da fasaha da ƙoƙarin jami’an tsaro, Filato ta fara dawo da sunanta a matsayin waje mai zaman lafiya da yawon buɗe ido.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan ta adda Boki Haram Muftwang
এছাড়াও পড়ুন:
IMF ta nemi Tinubu ya kyautata rayuwar talakawan Najeriya
Asusun Bada Lamuni na Duniya (IMF), ya buƙaci Gwamnatin Najeriya da ta tabbatar da cewa manufofin tattalin arziƙin ƙasar sun kare muradun mutane masu rauni.
Daraktar Hulɗa da Jama’a na IMF, Julie Kozack, ta bayyana hakan a yayin wata ganawa da manema labarai a birnin Washington, D.C.
NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansu Uromi: Barau ya ziyarci iyalan waɗanda aka kashe, ya ba su kyautar N16mTa jaddada muhimmancin bai wa talakawan Najeriya masu fama da ƙuncin rayuwa tallafin kuɗi sakamakon sauye-sauyen tattalin arziƙi.
Aminiya ta ruwaito cewa cire tallafin man fetur, wanda IMF ta ba da shawara a kai, ya haifar da tashin farashin man fetur daga kimanin Naira 200 kan kowace lita zuwa sama da Naira 1,000.
Wannan sauyi ya jefa ’yan Najeriya da dama cikin matsananciyar wahala.
Duk da haka, Kozack ta amince da ƙalubalen da jama’a ke fuskanta kuma ta jaddada buƙatar tallafa wa masu ƙaramin karfi.
Ta buƙaci gwamnati da ta mayar da hankali kan shirye-shiryen jin daɗin al’umma, kamar bayar da tallafin kuɗi, tare da inganta hanyoyin tara kuɗaɗen shiga na cikin gida.
Haka kuma, ta sanar da cewa jami’an IMF za su ziyarci Najeriya nan ba da daɗewa ba domin nazarin manufofin tattalin arziƙi na shekarar 2025 a ƙarƙashin shirin bincike na ‘Article IV’, wanda ke tantance yanayin tattalin arziƙin ƙasashe mambobin IMF.