Jami’ar Bayero Ta Kaddamar da shirin amfani da adaidaita Sahu wajen zirga zirga a Jami’ar
Published: 3rd, April 2025 GMT
Jami’ar Bayero Ta Kaddamar da shirin amfani da adaidaita Sahu wajen zirga zirga a Jami’arA wani gagarumin yunkuri na bunkasa zirga zirga da walwalar dalibai, Shugaban Jami’ar Bayero Kano Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya kaddamar da shirin amfani da babura masu kafa uku ko adaidaita a harabar jami’ar a hukumance.
Wannan yunƙurin na nufin samar wa ɗalibai da ma’aikata hanyar sufuri mafi aminci, mafi dacewa, da sauƙaƙe ƙalubalen da ke tattare da zirga zirga tsakanin sassan jami’ar.
Shugaban jami’ar wanda ya samu rakiyar magatakarda Haruna Aliyu da mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Haruna Musa da shugaban dakin karatu na jami’ar Dr. Kabiru Dahiru Abbas da shugaban hulda da jama’a na jami’ar Lamara Garba da Farfesa Yakubu Magaji Azare, Shugaban jami’ar ya jaddada kudirin hukumar ta BUK na ba da fifiko ga walwalar dalibai.
“Wannan shiri wani bangare ne na kokarin da muke yi na inganta tsaro da walwala ga dalibanmu.
Mun himmatu wajen sanya cibiyoyin karatunmu ba wai kawai su karfafa ilimi ba har ma da kwanciyar hankali da aminci ga kowa da kowa,” in ji Farfesa Abbas.
Ya kuma tabbatar wa da al’ummar jami’ar cewa za a yi amfani da kekunan ne ta hanyar sanya ido da kuma tantancewa, tare da horar da direbobin yadda ya dace su gudanar da aikin su a harabar jami’ar daga karfe 7 na safe zuwa 9 na dare.
Shugaban jami’ar ya kara da karfafawa dalibai cewa su yi amfani da wannan damar tare da kasashin za a kara yawan daidaita din domin biyan bukatun daliban da ma’aikata
Wannan ci gaban ya biyo bayan dokar hana babura da jami’ar ta yi a watan Fabrairun 2025 saboda matsalolin tsaro.
Gabatar da kekuna masu kafa uku ya fi aminci, kuma ingantaccen tsari ne da zai tabbatar da zirga zirga cikin harabar jami’ar cikin kwanciyar hankali.
Khadijah Aliyu Kano
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Bayero Shugaban Jami ar Shugaban jami ar
এছাড়াও পড়ুন:
BUK Ta Ƙaddamar Da Shafin Intanet Da Ɗalibai Za Su Ke Duba Sakamakon Jarrabawa
Duk da haka, ɗalibai masu kammala makaranta sai sun jira amincewar Majalisar Jami’ar kafin su samu damar duba sakamakonsu.
Ana sa ran wannan ci gaba zai inganta ayyuka a Jami’ar da kuma sauƙaƙa wa ɗalibai gudanar da harkokin karatunsu cikin sauƙi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp