Bello Turji ya kashe manoma 11 a wani sabon hari a Sakkwato
Published: 3rd, April 2025 GMT
Ƙasurgumin ɗan bindiga, Bello Turji, da mayaƙansa sun kai mummunan hari garin Lugu da ke Ƙaramar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato, inda suka kashe manoma 11.
Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne yayin da Turji ke dawowa daga wata ziyarar sallah da ya kai yankin.
Najeriya ta yi kuskuren barin Boko Haram ta yi ƙarfi — Muftwang NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansuWani mazaunin Isa, Basharu Altine Giyawa, ya ce, “Tun a ranar Asabar muka samu bayanai cewa Turji zai ziyarci Gatawa, kuma mun sanar da hukumomi.
“Duk da haka, shi da mutanensa sun bi ta ƙauyukanmu, sun yi bikin sallah, sannan suka kashe manoma 11 a hanyarsu ta komawa Fakai.”
Ɗan majalisar dokokin Jihar Sakkwato mai wakiltar yankin, Hon. Aminu Boza, ya tabbatar da samun rahoton harin.
Amma ya ce: “Turji bai ziyarci kowace unguwa a yankina domin yin sallah ba. Mun ɗauki matakin gaggawa bayan samun bayanai, wanda hakan ka iya zama dalilin da ya sa ya mayar da martani kan waɗannan manoman a Isa.”
Mazauna yankin sun bayyana damuwa kan yadda hare-haren ‘yan bindiga ke ci gaba da ƙaruwa, duk da ƙoƙarin jami’an tsaro.
Sun yi kira ga gwamnati da ta ƙara ƙaimi wajen magance matsalar domin kare rayuka da dukiyoyinsu.
Hukumomin tsaro har yanzu ba su fitar da wata sanarwa kan harin ba, amma majiyoyi sun bayyana cewa sojoji na bin sahun Turji domin daƙile ayyukansa a yankin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗan Bindiga hari Sakkwato
এছাড়াও পড়ুন:
Kotu A Kano Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Wani Matashi Da Ya Kashe Ƙanwarsa Da Kishiyar Mahaifiyarsa
A hukuncin da ta yanke, Mai Shari’ar ta ce, “Shaidun da masu gabatar da kara suka gabatar na da inganci kuma masu gamsarwa ne, don haka kotun ta samu wanda ake tuhuma da laifi kuma ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.”
A cewar mai gabatar da kara a karkashin jagorancin Lamido Abba-Sorondinki, lamarin ya faru ne a ranar 7 ga watan Janairu, 2023, a unguwar Rijiyar Zaki da ke Kano.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp