INEC ta yi watsi da buƙatar yi wa Sanata Natasha kiranye
Published: 3rd, April 2025 GMT
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana cewa buƙatar da wasu suka shigar don yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Mazaɓar Kogi ta Tsakiya kiranye, bai cika sharuɗa ba.
INEC ta ce yunƙurin bai cika sharuɗan Sashe na 69(a) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanadar ba.
Bello Turji ya kashe manoma 11 a wani sabon hari a Sakkwato NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansuWannan sanarwa ta fito ne daga shafukan sada zumunta na INEC a ranar Alhamis, 3 ga watan Afrilu, 2025.
Wasu ƙungiyoyi sun yi ƙoƙarin yi wa Sanata Natasha kiranye, wanda suka ce Sanatan na neman jefa su cikin rikicin da ka iya hana su samun romon dimokuraɗiyya.
Ƙungiyoyin sun miƙa ƙorafinsu ga INEC bisa hujjar cewa ba ta yi musu wakilci mai kyau ba.
Sun yi iƙirarin tattara sama da sa hannun mutum 250,000 daga cikin masu kaƙa ƙuri’a kimanin 480,000 da ke yankin.
Sanata Natasha, ta fuskanci ƙalubale a siyasa a baya-bayan nan, ciki har da dakatarwar tsawon watanni shida d Majalisar Dattawa ta yi mata bisa zargin aikata rashin ɗa’a.
Ta ƙalubalanci wannan hukunci, inda ta bayyana cewa an dakatar da ita ne saboda zargin cin zarafi da ta yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.
Wannan batu ya haddasa muhawara mai zafi kan haƙƙin mata da yanayin siyasar Najeriya.
Yadda INEC ta yi watsi da buƙatar tsige ta na nuni da tsauraran sharuɗan da ake buƙata kafin batun kiranye ya samu ƙarbuwa.
Wannan yana jaddada yadda ake buƙatar bin dokoki da tsari kafin a iya aiwatar da yi wa wani ɗan majalisa kiranye.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: kiranye Majalisar Dattawa
এছাড়াও পড়ুন:
Batun na yanke jiki na faɗi ƙarya ce — Wike
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewar ya yanke jiki ya faɗi har aka kai shi asibiti a ƙasar waje.
Ya ce wannan ƙarya ce da maƙiyansa na siyasa suka ƙirƙira don kawar da hankalin mutane.
NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta Fitaccen malami Dokta Idris Dutsen Tanshi ya rasuWike, ya yi wannan bayani ne a Abuja a ranar Alhamis yayin da ya kai ziyara wajen wani aiki da ake shirin ƙaddamarwa a watan gobe domin bikin cikar Shugaba Bola Tinubu shekara biyu a mulki.
A wata sanarwa da daraktan yaɗa labaransa, Anthony Ogunleye, ya fitar, Wike ya ce waɗanda ke yaɗa wannan labari suna ƙoƙarin juyar da hankalin jama’a daga batun da tsohon shugaban ma’aikatan Jihar Ribas ya fallasa na yunƙurin saka bam a majalisar dokokin jihar da kuma hari kan kadarorin gwamnati.
“Babu inda na yanke jiki na faɗi, balle har a fitar da ni zuwa ƙasar waje.
“Ko a ranar da Shugaba Tinubu ya yi buɗa-baki kan zagayowar ranar haihuwarsa na halarta.
“Haka kuma, a ranar Sallah na jagoranci mazauna Abuja zuwa taya shi barkar da sallah. Ba zan damu da irin waɗannan jita-jitar siyasa ba, kuma ba za su hana ni aiki ba,” in ji Wike.