Ƙoƙarin Tsige Sanata Natasha Ya Gaza Cika Ƙa’idar Doka – INEC
Published: 3rd, April 2025 GMT
Hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta bayyana cewa takardar neman tsige Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta tsakiya a Majalisar Dattawa, ba ta cika sharuɗɗan doka da kundin tsarin mulki ya tanada ba.
INEC ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa takaitacciya da ta wallafa a shafinta na Facebook yau Alhamis, tana cewa: “Takardar neman tsige Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya ba ta cika sharuɗɗan da ke cikin sashi na 69(a) na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 ba.
Sai dai hukumar ta yi alƙawarin fitar da cikakken bayani kan wannan ci gaba nan ba da jimawa ba.
Rahoton wakilinmu ya nuna cewa har yanzu ba a tabbatar ko masu ƙorafin za su samu damar gyara takardar domin dace wa da doka ko kuma za a yi watsi da ita gaba ɗaya ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Falasdinawa Da Dama Sun Yi Shahada A Yau Talata
A daidai lokacin da sake bude yaki a Gaza ya cika kwanaki 57,sojojin HKI suna ci gaba da kai hare-hare akan al’ummar Gaza da hakan ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa da dama.
Cibiyar watsa labaru ta Falasdinu ta sanar da cewa; Sojojin na HKI sun kai hare-hare masu yawa a sassa mabanbanta na gaza wanda ya fara tun daga watan Maris, da hakan ya kara jefa Falasdinawa cikin wahala, bayan yunwar da suke fama da ita.
Da safiyar yau Talata sojojin na HKI sun kai hare-hare sau 3 a garin Abasan a gabashin Khan-Yunus.
A cikin birnin Gaza kuwa sojojin na HKI sun baje wasu gidaje da kasa a karo na uku.
A garin Khan-Yunsu wani matashi mai suna Amid Hamdun al-Qudrah, ya yi shahada.
A unguwar “Shuja’iyyah” ma wani Bafalasdine mai suna Muhammad Mu’in al-Ja’abari ya yi shahada sanadiyyar raunin da ya samu a harin baya.
A unguwar “Zaytun” kuwa sojojin na HKI su kai hare-hare ne har sau 8 a yau Talata.
A daren jiya wasu Falasdinawa 3 daga iyali 1 sun yi shahada a cikin tantin ‘yan hijira a yankin ‘al’amudi’ a arewacin Gaza.