‘Yan Aware Na Taiwan Za Su Fuskanci Karin Hukunci Matukar Ba Su Daina Ba
Published: 3rd, April 2025 GMT
A jiya Laraba 2 ga wata, rundunar sojojin ‘yantar da al’umma ta kasar Sin ko PLA shiyyar gabashin kasar, ta kaddamar da wani atisayen soji mai taken “Strait Thunder-2025A”, a yankunan tsakiya da kudancin zirin Taiwan, wanda ya kasance matakin da aka dauka dangane da kalamai na shirme da jagoran yankin Taiwan, Lai Ching-te ya furta a kwanakin baya, da ma yunkurin jam’iyyar DPP da ke karkashin jagorancinsa na neman ‘yancin kan yankin Taiwan.
Duk da haka, wasu ‘yan tsirarrun kasashen yamma da ma kungiyoyi sun sake fitowa suna kara wa miya gishiri a kan batun, inda suka ce wai suna kin amincewa da daukar matakin kashin kai na canza yanayin da ake ciki a zirin tekun Taiwan. To, bari mu duba irin yanayin da ake ciki yanzu a zirin Taiwan. Sakamakon sa hannun wasu kasashen waje, har yanzu ba a kai ga tabbatar da dinkewar babban yankin kasar Sin da yankin Taiwan ba, kuma duk da haka, yadda babban yankin kasar Sin da ma yankin Taiwan ke karkashin ikon kasar Sin guda daya bai sauya ba, lallai wannan shi ne ainihin yanayin da ake ciki a zirin tekun Taiwan.
A hakika, wadanda ke mara wa Lai Ching-te baya su ne suke sa hannun wargaza kwanciyar hankalin zirin tekun Taiwan. Sai dai ko kadan kasar Sin ba za ta yarda da ballewar yankin Taiwan daga cikinta ta kowace hanya ba. ‘Yan aware na Taiwan za su fuskanci karin hukunci matukar ba su yi wa kansu kiyamul-laili sun daina ba. Hakan nan ma wadanda ke mara wa Lai Ching-te baya, za su girbi abin da suka shuka, idan suka ci gaba da keta ka’idar kasar Sin daya tak a duniya da kuma ma tsoma baki cikin harkokin gidan kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: yankin Taiwan
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka Ta Daba Wa Kanta Wuka Bisa Karin Harajin Da Ta Yi
Sanin kowa ne, ciniki mai inganci na bukatar kasuwa mai ‘yanci, da takarar da ake yi cikin daidaito, gami da manufa mai dorewa. Idan kasar Amurka ta ki samar da wadannan abubuwa, to, babu wani abun da za a yi, in ban da mai da kasar saniyar ware, da kara tabbatar da hadin kai tare da sauran abokan hulda. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp