Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-04-24@16:07:08 GMT

Gwamnatin Jigawa Ta Yi Sabbin Nade-nade A Fannin Ilimi

Published: 3rd, April 2025 GMT

Gwamnatin Jigawa Ta Yi Sabbin Nade-nade A Fannin Ilimi

Gwamna Umar Namadi ya amince da naɗin Dr. Jummai Ali Kazaure a matsayin sabuwar shugabar Kwalejin Ilimi, Shari’a da Nazarin Addinin Musulunci (JSCILS) da ke Ringim.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar.

A cewarsa, kafin wannan naɗi, Dr.

Jummai ta kasance malama a Kwalejin Ilimi ta Jihar Jigawa da ke Gumel. Tana da digiri na uku (Ph.D.) a fannin Gudanarwa da Tsare-tsare, tare da gogewa a harkar koyarwa daga matakin firamare har zuwa manyan makarantu.

“Dr. Jummai ta rike mukamai da suka gada da Darakta a Makarantar Sakandaren gwamnati ta ‘yan mata da ke Kazaure da kuma Darakta a Makarantar Sakandare ta larabci da ke Babura. Mace ce mai  kishin jasa da son cigaban ilimi da hidima ga al’umma,” in ji Sakataren Gwamnati.

Haka kuma, Gwamna Namadi ya amince da naɗa Hassan Nayaya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Raya Ilimi ta Jihar Jigawa (JERA).

“Kafin wannan mukami, Nayaya ya kasance mukaddashin Shugaban Hukumar. Ya samu digiri a fannin Lissafi daga Jami’ar Bayero da ke Kano a shekarar 2000. Ya fara aiki a ma’aikatar ilimi ta Jihar Jigawa ne tun daga shekarar 1992, har ya kai matsayin Darakta a shekarar 2020,” in ji sanarwar.

Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa waɗannan naɗe-naɗen suna daga cikin kokarin Gwamna na inganta shugabanci a fannin ilimi da ci gaban al’ummar Jihar Jigawa.

Sanarwar ta ƙara da cewa, an yi naɗin ne bisa cancanta, kwarewa da nagarta.

“Yayin da ake taya sabbin shugabannin murna, ana fatan za su yi aiki tukuru domin ba da gudunmawa ga ci gaban Jihar Jigawa.”

Sanarwar ta ƙara da cewa dukkan naɗe-naɗen sun fara aiki nan take.

 

Usman Muhammad Zaria 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa Jihar Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Inuwa Ya Bayar Da Gudunmawar Naira Miliyan 10 Ga Iyalan Wadanda Hatsarin Ista Ya Rutsa Da Su A Gombe

Da yake jawabi a fadar Mai Tangele (Sarkin Billiri), Danladi Sanusi Maiyamba, ya bayyana lamarin da matukar bakin ciki tare da fatan samun makoma mai kyau ga wadanda suka rasu, ya kuma warkar da wadanda suka samu raunuka da gaggawa.

 

Daga nan sai Gwamna Inuwa ya sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan 2 kowanne ga iyalai biyar da suka rasa rayukan ‘yan uwansu, wanda ya kai adadin zuwa Naira miliyan 10.

 

Ya kuma yi alkawarin biyan kudaden jinya ga wadanda ke karbar magani a Asibitocin jihar.

 

A yayin da yake godiya, Sarki Maiyamba ya ce, hatsarin na Easter ya girgiza daukacin masarautar Tangale, amma ya amince da matakin da gwamnatin jihar ta dauka, wanda ya ce hakan ya taimaka wajen hana barkewar rikici a yankin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yobe na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya mafi zaman lafiya – Buni
  • Gwamnatin Kano Da NBC Sun Shirya Taron Bita Domin Tsaftace Harkar Siyasa
  • An Bayyana Filin Jirgin Sama Minna a Matsayin Mafita Ga Jiragen da ke sauka Abuja
  • Jirgin Farko Daga Minna Zuwa Abuja Ya Nuna Haɗin Gwiwar Gwamnatin Tarayya Da Jihohi – Minista
  • Gwamna Inuwa Ya Bayar Da Gudunmawar Naira Miliyan 10 Ga Iyalan Wadanda Hatsarin Ista Ya Rutsa Da Su A Gombe
  • Gwamna da jiga-jigan siyasa a Delta sun fice daga PDP zuwa APC
  • Amurka ta kakaba wa Iran sabbin takunkumai duk da tattaunawa
  • Rashin Tsaro: Gwamnatin Neja Ta Saka Dokar Zama A Gida A Minna
  • Sin Na Hasashen Samun Karin Yabanya A Shekarar 2025
  • Inganta Kiwon Lafiya: Gwamna Buni Ya Ziyarci Sashen Koyar Da Kwararrun Likitoci A Damaturu